Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 7 da suka bambanta Aisha Buhari da matan tsofaffin shugabanni
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Aisha ita ce uwargidan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari wadda ta yi fice kamar sauran takwarorinta da suka gabata.
Sai dai a bangaren Aisha, a iya cewa akwai wasu abubuwa da dama da suka bambanta ta da sauran matan tsofaffin shugabannin kasar, musamman wadanda aka fi sani kamar su Maryam Babangida da Maryam Abacha da Stella Obasanjo da Turai 'Yar aduwa da kuma Patience Jonathan.
Kusan dukkan wadancan matan tsaffin shugabannin sun yi tarayya da kamanceceniya a al'amura da dama amma sun sha bamban da Aisha Buhari a wadansu abubuwan.
BBC ta yi nazari kan abubuwa bakwai da suka bambanta Aisha Buhari da wadancan takwarori nata.
1- Sukar gwamnatin da mijinta ke jagoranta a bainar jama'a
A bayyane take cewa ba a taba samun matar wani shugaban Najeriya da ta taba fitowa bainar jama'a ta soki gwamnatin mijinta ba.
Za a iya cewa duk matan shugabannin da suka gabata kansu hade yake da mazajensu kuma bakinsu daya a kowane yanayi.
A watan Disambar 2016 ne Aisha Buhari ta fara fitowa bainar jama'a ta soki tsarin gwamnatin mijinta a wata hira da BBC Hausa.
A cikin hirar ne dai uwargidan shugaban kasar ta gargadi mijinta da cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba, idan har al'amura suka ci gaba da tafiya yadda suke ba, inda ta ce gwamnatin mai gidanta ta yi watsi da fiye da rabin mutanen da suka yi masa wahala har ya samu mulki.
Wannan hira ta tayar da kura ba ma a Najeriya ba kadai ba har ma a wasu kasashen waje. Ba a taba samun wata matar shugaban kasa da ta yi haka ba a baya.
Al'amarin ya zo wa mafiya yawan 'yan Najeriya a ba-zata don ba a taba ganin matar wani shugaban kasa ta fito gaba-gadi ta yi irin hakan ba, musamman a wata babbar kafar yada labari ta kasar waje, saboda watakila tana ganin kafofin cikin gida ba za su samu kwarin gwiwar yada hirar ba.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Aisha Buhari ta shammaci ma'aikatan fadar shugaban kasar ne, inda har aka shiga aka yi hirar ba su sani ba. Ita kanta BBC a wancan lokacin ta sha matsin lamba kan ta janye hirar.
Baya ga wannan hira, Aisha ta kuma taba jan kunnen jam'iyyar mijinta ta APC kan rabon mukamai.
Wannan halayya ta sa a wani lokacin har an taba baza labaran karya kan sauke alkalin-alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, inda aka ce ta yi Allah-wadai da matakin mijinta, sai dai Aisha ta musanta hakan.
2- Rufe ofishin matar shugaban kasa
A kundin tsarin mulkin Najeriya babu ofishin matar shugaban kasa, amma kuma gwamnatocin baya sun bude ofishin tare da yi masa gata, wata al'ada da aka dade ana shan romonta.
Ba a ware wa ofishin kudi a kasafin kudin kasar, sai dai ma'aikatar mata ce ke ware kudin da ake kula da shi.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa a shekarar 2014 Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai soke ofishin First Lady idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Kuma har ya zuwa yanzu a wa'adin mulkinsa na biyu babu wannan ofishi a hukumance.
Wannan lamari ya yi matukar bambanta Aisha da sauran takwarorinta da suka gabata, duk da cewa dai ita ma tana da wani shiri da ta kirkiro na Future Assuredkamar yadda Maryam Babangida ta kirkiriBetter Life, da Family Support Programme na Maryam Abacha da na Turai 'Yar Adua Women And Youth Empowerment Foundation WAEPda na Stella Obasanjo Childcare Trust da kuma na Patience Jonathan Women For Change Initiative.
3- Rashin ta ce a al'amuran mijinta
Haka kuma wasu al'ummar kasar da dama na ganin cewa Aisha ba ta da isasshen fada a ji a wajen Shugaba Buhari, musamman ganin cewa a hirar da ta yi da BBC a wancan lokaci ta yi hannunka mai sanda da cewa wasu mutane sun kankane komai.
Lokacin da Buhari ya yi jinya a London, ba su tafi tare da mai dakinsa ba sai daga baya ta je. Wani lamarin da yasa wasu 'yan kasar ke sanya alamar tambaya.
Ba kamar takwarorinta da suka gabata ba, irin su Turai, wadda a lokacin da mijinta marigayi shugaba Umaru Muasa 'Yar aduwa ya yi doguwar jinya a Saudiyya, ita ce gaba-gaba wajen jinyarsa. Har ma wasu rahotanni na cewa sai wanda ta so yake ganinsa cikin manyan mukarrabansa da ke zuwa duba shi.
4- Tata-burza tsakanin ta da dangin miji
Mata da dama ne a duniya za a ce suna da matsala da dangin miji, amma na wata ya fi na wata fitowa fili, ko da kuwa babban gidan ne ana samun hakan.
Duk da cewa babu tabbas ko matan tsofaffin shugabannin Najeriya suna da matsala da dangin mazajensu ko babu, to ba ta dai fito fili ba.
Amma a bayyane take cewa akwai takun saka tsakanin Aisha da dan yayar Buhari Mamman Daura da iyalansa.
Wanann abu ya sa 'yan Najeriya na ganin sa wani bambarakwai da ba a taba gani tsakanin iyalan wani shugaba da danginsa ba.
Ana ganin wasu da ke da kusanci da shugaban kasar na hana Aisha rawar gaban hantsi har a cikin gidanta, abin da babu wata matar shugaban Najeriyar da ta taba cin karo da shi.
Sai dai iyalan Daura ta bakin 'yarsa Fatima sun musanta hakan, duk da cewa kuwa Aishar ta sha yin shagube ga wasu mutane uku da ake ganin har da Mamman Daura a cikinsu.
5- Kuruciya
Duk da cewa Maryam Babangida sun dare mulki lokacin da take 'yar shekara 37, wato kenan ta fi Aisha kuruciya, to matar Buharin ce ta biyu a jeri wadanda suka fi karancin shekaru cikin matan sauran shugabannin da suka gabata.
Sai dai watakila salon kuruciyar Aisha ya bambanta musamman duba da zamanin da suke nasu mulkin, musamman zamani na bazuwar intanet da kafafen sada zumunta.
"Aisha akwai kuruciya kuma akwai kyau, kuma wannan kuruciya ta sa ta bambanta da takwarorinta da suka wuce," in ji Rahma Abdulmajid mai sharhi da kuma rajin kare hakkin mata.
Wannan kuruciya ta Aisha ce ake ganin ya sa ta zamo mai yawan jawo ce-ce-ku-ce a mulkin mijinta, kamar sukar wasu manufofin gwamnatin.
Sannan wasu na ganin takamar kuruciyarta ke sa yanayin suturarta yake dan bambanta da na takwarorinta na baya, musamman Maryam Abacha da Turai 'Yar adua, inda ita Aisha a wasu lokutan ke sa kananan kaya kuma na kawa wato (designers), sannan hakan yana tayar da kura.
Amma duk da haka ba za a ce ta wuce Maryam Babangida a gayu ba, sai dai kawai Aisha ta zo a zamanin da aka kara samun wayewa sannan gayu ya kara samun tagomashi a duniya.
6- Aji
Rahama Abdulmajid ta ce wani abu da halayyar Aisha da ya sa ta zama daban shi ne "ajinta".
"Ita mace ce da take ganin ba da bazar mijinta kawai za ta yi rawa ba, tana jin tana da aji kuma za ta iya duk abin da ta ke so saboda wayewarta da kwazonta da kwarewarta ta wasu fannonin.
"Tana ganin ba za ta yi shiru ba ta ga gwamnatin mijinta ba ta yi wa 'yan Najeriya abin da ta yi alkawari.
"Wannan dabi'u ne na musamman (special personality) da kuma aji da ba kowace mace ake samun irinsu a tare da ita ba."
7- Rashin boye matsalar cikin gidanta
A ganin wasu da dama Aisha Buhari ta bambanta da sauran takwarorinta da suka gabata ta wajen kasa boye abubuwan da ke faruwa a gidanta.
"Duk da cewa dai dama asirin babban gida bai cika rufuwa ba, amma a nata bangaren ana iya karanto cewa tana cike da wata damuwa da lallai ba a san dalilinta ba, sai dai ba za ta rasa nasaba da gidanta ba," in ji Rahama.
"Ko a kwanan nan a hirar da ta yi da manema labarai ranar da ta dawo daga Ingila bayan shafe watanni, an tambaye ta batun jita-jitar auren shugaban, amma sai ta kada baki ta ce ita wadda za a auran ai ba ta fito ta karyata ba.
"Da jin wannan kalami ai ka san cikin kishi irin na mata aka yi shi, kuma ga alama akwai abin da ke damunta mai alaka da gidan aurenta. Ai ba a taba ganin irin hakan a tattare da wata matar shugaban kasa ba.
"Misali Patience Jonathan ai an sha rade-radin cewa mijinta na soyayya da ministarsa Diezani Alison Maduekwe, amma ai duk baram-baramar Patience ba ta taba nuna alama ba. A cewar mai rajin kare hakkin matan.
"Amma mun sha jin cewa ta tabbatar da toshe duk wata kafa da zata bai wa Diezani damar kebewa da mijinta ko cikin sha'anin aiki," in ji Rahama.
Rufewa
Ganin cewa akwai sauran shekaru uku kafin wa'adin mulkin Shugaba Buhari na biyu ya kare, wasu masu sharhin na ganin cewa ba lallai ne ace an ga karshen abubuwan da suka fito fili wadanda kuma suka kara bambanta Aisha da matan tsaffin shugabannin Najeriyar ba.