Amurka ta kakaba wa ma'aikatun Turkiyya takunkumi

Gwamnatin Amurka ta saka wa wasu ma'aikatun gwamnati da wasu manyan jami'an gwamnatin Turkiyya takunkumi a wani martani kan ahre-haren da Turkiyyar ke kai wa arewacin Syria.

Shugaba Donald Trump ya kuma kira takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan inda ya nemi a tsagaita wuta ba da bata lokaci ba.

Sojojin Syria dai sun isa wasu yankuna da ke arewa maso gabashin kasar, kuma wannan na iya haifar da wani fito-na-fito tsakanin dakarun gwamnatin Syria da na Turkiyya.

Shiga sojojin Syria wannan yankin ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka kulla ne tsakanin dakarun Kurdawa da na Syrian bayan da Amurka ta juwa wa Kurdawan baya.

Turkiyya ta ce tana kai wadannan hare-haren ne saboda ta mayar da 'yan Syria kusan miliyan biyu can bayan ta samar da abin da ta kira "yankin tsaro", wanda zai kai fadin kilomita 30 cikin Syria daga kan iyakarta.

A halin yanzu akwai miliyoyin 'yan Syria da ke gudun hijira a Turkiyya.

Amma yawancin 'yan gudun hijiran ba Kurdawa ba ne, kuma wasu na ganin wannan matakin na Turkiyya na iya haifar da wata matsalar - wato Kurdawan na iya rasa muhallansu da garuruwansu gaba daya.