An sace shugaban makaranta a Kaduna

Asalin hoton, FACEBOOK/NASIR EL-RUFA'I
A jihar Kaduna da ke Najeriya iyalai da kuma mazauna yankin Kajuru sun tabbatar da wani hari da 'yan bindiga suka kai, tare da yin awon-gaba da shugaban wata kwalejin ilimin kere-kere da ke yankin.
Mai dakinsa Amina ta bayyana wa BBC cewa 'yan bindigar sun tafi da shugaban makarantar ne mai suna Francis Mazi, bayan sun lakada masa duka.
Har yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan lamarin.
Bayanai sun bulla a kafofin yada labarai na Najeriya, inda rahotanni suka ce mazauna yankin sun ji karar harbe-harbe a cikin kwalejin, kuma daga baya aka tabbatar da sace shugaban makarantar.
Mai dakinsa Amina ta ce "maharan sun shigo ta kofar baya, kuma shi mai gidan sai ya shiga daki ya kulle kansa amma suka sassare kofar har sai da ta balle.
"Sun yi ta maganganu har wasu na cewa a kashe shi. Sai suka bi shi da gudu suka yi masa duka, har sun kai wani wuri kuma sai suka dawo suka dauki rigarsa suka tafi" in ji ta.
Ta ce masu garkuwa da mutanen sun tuntube ta kuma sun bukaci ta biya naira miliyan ashirin kafin a sako mijin nata.
A cikin makon nan a shalkwatar rundunar 'yan sanda da ke cikin garin Kaduna, rundunar ta baje wasu mutane da ta ce an kama su ne bisa zargin su da aikata laifuka daban-daban, wadanda suka hada har da satar mutane domin neman kudin fansa, abinda ya yi kamari a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Ali Aji Janga, ya shaida wa manema labaru cewa rundunarsa ta gano wurin da ake rike da dalibai 6 da malamansu 2 na kwalejin Engravers da aka sace a makon da ya gabata.
Sai dai ya ce rundunar ta gwammace ta bi hanyoyi na sulhu wajen karbo su maimakon yin amfani da karfi, wanda ka iya yin illa ga lafiyarsu.











