Yadda ake shigar da wiwi daga Benin da Ghana zuwa Najeriya

- Marubuci, Umar Shehu Elleman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Lagos
Hukumar yaki da fasa kwauri a Najeriya, ta kama tabar wiwi ta kimanin naira miliyan dari daya da sittin (N160, 000.000), a dab da a bakin iyakar Naijeriya da jamhuriyar Benin.
Wannan dai shi ne kame mafi girma kuma na farko da rundunar ta yi, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta kulle bakin iyakokin kasar da makwabtan kasashe.
Kontirola Zhilkiflu Abdullahi wanda ke kula da rundunar a jihohin Oyo da Osun ya ce ``an kama tabar wiwi bayan an shigo da ita daga Ghana zuwa Jamhuriyar Benin har ta shigo Najeriya``.
Kontirola Zhulkiflu ya kuma ce ``abar wiwi da ke kunshe cikin sinki-sinki da kuma a cikin buhu-buhu, an yi badda sawu kamar dai an dauko dusar katako ce."
To amma bayan bincike sai rundunar ta gano tabar wiwi ce da aka yi safararta zuwa Najeriya; kamar dai yadda ma su safararta ke cewa akwai mashayanta da yawa a Naijeriya.
Wannan ne dalilinsu na mayar da kasar zangon mashayan tabar wiwi.

Gwamnatin Naijeriya, ta toshe bakin iyakokinta da sauran kasashe ta tudu, da manufar hana harkokin shige da fice na kayayyaki .
Darajar kudin tabar wiwi da aka kama a baya-bayan nan ta kai kimanin naira miliyan 160 da rundunar ta yi a wadannan jihohi.
Jami'an rundunar ce dai su ka kama ganyen wiwin a cikin dajin Elekokan /Ofegun cikin karamar hukumar Iwajowa da ke da kudancin kasar da jamhuriyar Benin.
Tun bayan kulle bakin iyakokin Najeriya 'yan kasuwa ke ta korafi cewa wannan mataki ya haifar musu da tawayar harkokin kasuwanci.
To sai dai Controller Zhulkiflu ya ce masu kukan rufe iyakar sun kasance wadanda ke amfani da iyakokin kasar, ba tare da an san abin da suka shiga ko fita da shi ba.











