Me ya sa aka sake kama Abdurrashid Maina?

Asalin hoton, FACEBOOK/ABDULRASHEED MAINA
Za a iya cewa Abdurrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon Najeriya da jami'an tsaron kasar sun kwashe shekaru hudu suna Allan-ba-ku Allan-karbe.
Kama daga jami'an hukumar EFCC da na DSS zuwa ga na 'yan sanda duk sun kama AbdulRasheed Maina a lokuta daban-daban.
A ranar Larabar nan ne mai magana da yawun hukumar DSS, DR Peter Afunnanya ya shaida wa manema labarai cewa jami'an hukumarsa da na EFFCC sun kai samame wani otal inda suka kama Abdurrashid Maina.
Dr Peter ya ce a lokacin da suka je otal din sun samu Mainan ne tare da dansa mai shekara 20 wanda ya yi yunkurin far wa jami'an da wata 'yar karamar bindiga da ke hannunsa, kafin daga bisani su ci karfinsa.
Mai magana da yawun DSS din ya kara da cewa jami'an nasu sun samu bindiga karama da alburusai da mota mai sulke kirar Range Rover da BMW da na'urar daukar hoto daga sama da kuma kudaden kasashen waje duka a tare da Abdurrashid Maina.
Hukumar DSS din ta ce za ta mika Maina tare da abubuwan da aka samu a tare da shi ga hukumar EFCC domin daukar matakin da ya kamata wajen hukunta shi.
Me masana ke cewa?
Masana da masu fafautukar ganin an dakile rashawa da cin hanci a Najeriya, irin su Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC na cewa ya kamata a gurfanar da Abdurrashid Maina a gaban kuliya domin tatance ko yana da laifi bisa zarge-zargen da ke kansa.
Ya ce idan an same shi da laifi ya kamata a hukunta shi dai-dai laifinsa, idan kuma ba a same shi da laifi ba sai a ba shi hakuri tare da wanke shi.
Rafsanjani ya kara da cewa ya kamata a kamo sauran mutanen da ake zargi da hannu a badakalar da ake zargin Abdurrashid domin hukunta su gaba daya ba tare da nuna banbanci ba.
Ana dai zargin Abdurrashid Maina ne da batan kudi sama da naira biliyan biyu cikin kudin yin garam bawul ga tsarin fanshon Najeriya, bayan da wani kwamitin majalisar dokokin kasar ya gudanar da bincike.
Me ya faru da Maina daga nan?
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta fara neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 dangane da zargin yin sama da fadin na naira biliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon kasar.
A wancan lokacin har zanga-zanga wasu suka yi zuwa majalisar dokokin Najeriya domin nuna goyona baya ga Abdulrasheed Maina.
Amma bai fito ya kalubalanci neman da ake yi masa ba.
Tun lokacin kuma ba a a sake jin duriyarsa ba sai lokacin da rahotanni suka ce ya koma aiki a ma'aikatar cikin gida ta Najeriya, a matsayin daraktan riko.
Amman ministan ma'aikatar cikin gidan, Abdulrahman Dambazau, ya ce shi bai san komai ba dangane da dawowar AbdulRasheed Maina aiki.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran ministan, Ehisienmen Osaigbovo, ya fitar ta ce daga ofishin shugaban ma'aikatan Najeriya ne aka turo Abdulrasheed aiki a ma'aikatar.
Saboda haka ministan bai san ya ya aka yi Abdulrasheed Maina ya dawo ma'aikatarsa ba.
A watan Oktoba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina, daga sabon mukamin mukaddashin darakta a ma'aikatar harkokin cikin gida.










