Za mu daukaka kara - Abba K Yusuf
Ku latsa hoton da ke sama domin ganin bidiyon
Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Kano, ya ce za su daukaka kara domin kalubalantar tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar Kano da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi.
Abba Kabir Yusuf ya shaida wa BBC cewa tuni lauyoyinsu suka cike dukkanin takardun da ake bukata na daukaka kara.