'Na kirkiri na'urar gano Maleriya bayan mutuwar dan uwana'

wanda ya kirkiri maleriya

Asalin hoton, iCog Labs

Wani dalibi dan kasar Habasha wanda ya kirkiri na'urar gane ko mutum na dauke da kwayar cutar Maleriya nan take ya fada wa BBC cewa masu zuba hannun jari na da na niyyar mara mashi baya duk da cewar ya gaza yin nasara a wata gasa ta kirkirar naurar gurza hoto ta 3D.

Torpout Nyarikjor, wanda dalibi ne a fannin koyan aikin injiniya a jami'ar Dilla da ke kudancin Habasha ya ce mutuwar dan uwansa wanda cutar Maleriyar ne tayi sanadi, ta zaburar da shi har ya kirkiri wannan naurar.

'' A lokacin da nake karami, na ga yadda yayana ya rasa ransa a sanadiyyar wannan cutar. A lokacin, na yi bakin ciki matuka kuma hakan ya sa nake da yakinin cewa, wata rana zan tsayar da faruwar hakan, sai dai ban san ta wace hanya ba, '' inji yaron dan shekara 24.

Cutar Maleriya na daukar rayukan yara fiye da 2,500 a kullum a nahiyar Afirka, a cewar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Na'urar Mista Torpout na da saukin amfani - Ana soka dan yatsa a cikin na'urar inda za ta gano ko jinin mutum na dauke da cutar ko kuma akasin haka.

''Ya ce, duk wanda ya iya karatu zai iya amfani da na'urar.

Hakan na nufin cewa za a iya shan maganin da zai warkar da Maleriya da wuri ta yadda mara lafiya zai rayu.

wanda ya kirkiri maleriya

Asalin hoton, Torpout Nyarikjor

A halin yanzu, sabuwar na'urar gano cutar Maleriya wadda ake kira ''Tor'' na da kashi 70% cikin 100 na tabbacin amsar da zai bayar, kuma dalibin wanda ke shekarar sa na hudu a jami'a na cigaba da gudanar da aikin akan na'uarar domin tabbatar da cikakken ingancin sa.

Na'urar ta lashe gasar kirkira a mataki na yankuna, wacce iCog Labs - wani kamfani da ke a babban birnin Addis Ababa, wandanda kuma suke aiki a kan basirar na'urori.

Sai dai kuma bai yi nasara ba a mataki na karshe a gasar wanda kuma anan ne ya rasa kyautar kudi har dala 3,400 (fam 2,700), wanda ya ce bai ji dadi ba saboda ya sa rai cewa, wannan kirkirar za ta kawo sauyi.

Duk da haka dai, yana da kwarin gwiwa a kan makomarsa a nan gaba.

''Buri na shine na zama mai daukar aiki ba wanda za'a dauka aiki ba, inji dan matashin wanda ya fito daga yammacin birnin Gambella.

Yana so ya koma mahaifarsa domin ci gaba da sauran ayyuka wanda zai sanya matasa masu ilimin fasaha a ciki, wadanda kuma ke da tunani irin nasa a kan yadda na'urar za ta sauya rayukan mutane.