Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tallafin Kwankwaso ya janyo muhawara
A ranar Talatar da ta gabata ne dai Gidauniyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta dauki nauyin wasu matasa 'yan asalin jihar, 242 domin karatun digiri na biyu a wata jami'a da ke kasar Indiya.
Dukkanin daliban suna da sakamako mai daraja ta daya a shaidar kammala digirinsu na farko daga jami'o'i daban-daban na Najeriya.
Rabi'u Kwnakwaso ya shaida wa BBC cewa sun kammala biya wa kowane dalibi daga cikin daliban fiye da 200 kudin karatu daga farko har zuwa kammalawa.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron abin da Kwankwaso ya shaida wa wakilin BBC na Kano, Khalipha Dokaji:
Tun dai da wannan labari ya bazu a fadin kasar musamman bayan da magoya bayan Sanata Kwankwaso suka baza batun a kafafen sada zumunta, 'yan kasar suka yi ta yin tsokaci, inda wasu ke yabo wasu kuma ke sukar al'amarin.
To sai dai wasu na sukar matakin bai wa matasa irin wannan tallafi saboda yadda suke sanya tufafin da ke alamata su da mutumin da ya ba su tallafin.
Shi wannan yana cewa ya san mutumin da ya bai wa "matasa fiye da 30 tallafin karatun digiri a unguwarsu ba tare da ya san su ba, amma kuma bai sa su su sanya wani nau'in tufafi ba."
Ku san za a iya cewa wannan ne karon farko da wani dan siyasa ba gwamnati ba kuma ba mai rike da mukamin gwamnati ba, yake daukar nauyin karatun matasa masu yawa haka, a bayyane.
To sai a ranar 24 ga watan Sautmba ne Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya nemi tallafi daga jama'a domin su zuba kudade a gidauniyar tasa da manufar tallafa wa daliban, inda ya yi wa wadanda suka tallafa din godiya.
A shafinsa na Twitter, Sanata Kwankwaso ya ce "muna mika godiya ga kowa da kowa bisa tallafa wa gidauniyar Kwankwasiyya mai ba da tallafin karatun digiri na biyu a kasashen waje...Muna godiya sosai da tallafin da kuke ba mu."