Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shirin rediyo da ya hada yara da 'yan uwansu a Rwanda
- Marubuci, Flora Drury
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wannana labarin wasu samari ne da suka kusa bacewa har abada a lokacin da mutane ke tserewa daga rikicin da ya dabaibaye kasar Rwanda a 1994.
Kuma labari ne kan tasirin rediyo wajen kawar da tsoro da damuwa domin isa ga wurare a gomman shekaru domin yaye wa yaran damuwa da kuma dawo da su gidajensu da sada su da iyalensu.
"Ya dawo mana da kyakkyawan fata a tsakaninmu," inji Theogene Koreger, dan shekara 25 a hirarsa da BBC bayan bacewar dan dan uwansa.
"Sakon ya isa wurin da ba za mu iya kaiwa ba - sun isar da sakon fiye da yadda muke yi."
Labarin ya fara ne bayan kisan kare-dangi na Rwanda. Kwana 100 na kashe-kashen da fyade ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 800,000 'yan kabilar Tusti da 'yan kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi.
Dubban daruruwan mutane kuma sun tsere daga gidajensu domin neman mafaka cikinsu har da kananan yara 120,000 da aka raba da iyayensu.
Mugabo da kanensa Tuyishimire na daga cikin kananan yara 40,000 da suka tsallaka iyakar kasar domin neman tsira. Kuma Mugabo dan shekara bakwai ya tsinci kansa a matsayin shugaban iyalan da suka rage shi da kanen nasa.
Bayan haka amanar da mahaifiyarsa ta ba shi a karshe kafin mutuwarta ita ce ta kula da kanensa Tuyishimire wanda a lokacin ya fara koyon tafiya.
Amma yanzu su ke kula da kansu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda suke fadi-tashin yadda za su rayu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kan iyakar Rwanda.
A wancan lokacin "muna iya rayuwa da barar tumatir ko gahawa," kamar yadda ya bayyana a shekara 25 bayan faruwar hakan, cikin alfahari da jarimta.
Amma sansanonin na hadari. Kimanin miliyoyin 'yan gudun hijirar da ke neman mafaka a can kan iya tsira daga kisan kare-dangi. Amma yanzu ana fama da cutar amai da gudawa da atini a sansanin.
karin wasu mutum 10,000 kuma na iya mutuwa kafin su koma gidajensu.
"Yanayin sansanonin ba shi da kyau ko kadan. Duk inda ka duba cututtuka ne," in ji Rene Mukuruwabu a zantawarsa da BBC a wani lambu a Kigali mai nisan kilomitoci daga inda shi da iyalensa suka tsinci kansu bayan sun tsere don dole.
Ana iya cewa Rene ya yi sa'a domin iyayensa na tare sadda suka isa Tanzania a 1994.
Amma daga baya mahaifinsa ya bace. Ita kuma mahaifiyarsa wadda a baya ta bude wata cibiyar kula da marasa lafiya ta gamu da ajalinta a sansannin.
Kafin ka ce komai sai shi da dan uwansa Fabrice da kuma 'yar ubansa kadai suka rage a cikin 'yan gidansu.
Sai wani lokaci kuma Rene dan shekara biyar ya sake gano 'yan gidansu.
Bayan karewar yakin a 1994, ma'aikatan agaji sun yi fama da matsalar kula da mutanen da suka samu rauni a ciyar da masu fama da yunwa da kuma samar da matsuguni ga wadanda suka rasa muhallansu.
Yaya za a sada kananan yaran da suka bace da iyayensu.
Yaya za a iya gano mutane da 'yan uwan wadanda suka tsere suka bari alhali a lokacin babu wayar salula kuma babu intanet, ga shi mutane sun tsere ba tare da sun dauki komai ba saboda tashin hankalin da kasar ke ciki?
"Shugaban sashen harshen Swahili na BBC a 1994, Neville Harms, shi ne ya ba da shawarar," in ji Yusuf Mugenzi. "Shi ya bude shirin sake hada iyalai da suka bace wa juna."
Sakamakon haka aka kirkiro da wani shirin minti 15 da BBC ke yadawa a Rwanda da kasashe masu makwabtaka da ita. Shirin kan fara ne da labaru sannan a sanya sunayen mutane da ke neman 'yan uwansu da dangi.
Gaskiya hada shirin na da wahala kuma ya kunshi yin aiki da kungiyar Red Cross, wacce ita ke daukar sauti sannan ta aika da kaset din a sanya a dakin gabatar da shirye-shirye.
"Daga nan sai mu sanya muryoyin da aka dauka daga sansanonin," in ji Mugenzi daya daga cikin masu gabatar da shirin.
Daga karshe a kan kira muryoyin da suna Gahuzamiryango (wato mai hada iyalai). An fara gabatar da shirin ne shekara 25 da suka gabata.
Da farko an tsara shirin ne na tsawon minti uku. Daga baya sai aka sauya hakan.
Karshen ganin Rene da iyayensa shi ne sadda suke kan hanyarsu ta zuwa Rwanda. Daga nan ba su kara haduwa ba.
"Shin za ka iya kaddara dan yaron da ya bace?" Ya tambaya. "Ina kuka, na yanke tsammani. Ina iya ganin mutane da yawa amma babu 'yan uwana cikinsu."
Ko a lokacin da ma'aikatan agaji suka dauke shi ba ya iya magana.
"Sun tambayi sunana da adireshina. Amma tsoro da fargaba da rashin yarda sun sa na kasa magana."
Sai da ya yi watanni bai kara iya magana ba yayin da yake kai-komo a wani gidan marayu da ke cike da yara kamarsa da su ma suka tsinci kansu su kadai a duniya.
Bayan ya fara samun nutsuwa a cikin sabbin 'yan uwan nasa - sai ga wata murya a rediyo.
"Makwabcina ya zo a guje yana fada mini cewa an kira sunana a rediyo," yana ba da labari. Ya ruga zuwa gidan makwabcin domin ya ji da sunan nasa da kansa.
"Ana kiran sunaye - sunana ne."
"Na kasa iya tuna sunana amma na tuna sunan kanena," in ji Mugabo lokacin da yake nuna wa BBC hoton wasu kananan yara da Red Cross ta gano suna rayuwa su kadai a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Hakan ya wadatar domin a Kigali ma kawunsu Theogene shi ma ya ji sanarwar da aka yi a rediyo.
"Da na ji an kira a rediyo sai na ji kamar daga sama," cikin murmushin dake nuna wanin irin farin cikin da bai taba ji ba a tsawon shekara 25.
"Saboda mutanen da ke nan a Rwanda ba su da hanyoyoin sadarwa, kuma ba mu samu sako daga ko'ina ba."
Jin sunayen shi ne farko daga cikin abubuwan da suka mayar da samarin gida bayan shekaru. Kasar na fama da rikici kuma hanyoyin na da matukar hadari.
Babban abun shi ne samarin na tsoron komawa gida.
"Na samu wasikar kawuna da ke Rwanda cewa yana son ganinmu. Amma na ce a'a ba zan koma ba", in ji Mugabo.
"Ina gani mahaifina da mahaifiyata suka mutu, saboda me zan koma?"
Akwai wani abu daya: kawunsa soja ne a rundunar 'yan tawaye ta RPF ta kabilar Tusti da suka kwace mulki domin kawo kisan kare dangi a Rwanda. A lokacin da Mugabo ke tasowa an nuna masa cewa sojojin kyankyasai ne masu wutsiya.
Daga nan abu daya ya rage wa kawun nasu. Sai kawun nasa ya aika masa da hotonsa da na 'yan uwansu. Bayan shekara daya a cikin jeji, sai Mugabo da Tuyishimire suka koma gida.
Rene ba zai iya cewa ga abin da ya hana shi yin komai ba a tsawon shekarun da ya rika ji ana kiran sunansa a rediyo ba.
Watakila tsoro ne. Ya san yana rayuwa cikin farin ciki da sabbin 'yan uwansa. Ba mamaki wannan ya fi masa kwanciyar hankali.
Duk da haka yana fatan wani na can yana nemansa.
"Ko da yaushe abin da nake tunani ke nan," in ji shi. "Ina so in kara ji a rediyo amma ba hali."
Hakan ta sa ya yi riko da sunansa, duk da cewa uwar rikonsa ta ce akwai yiwuwar ya sauya suna saboda ya saje a cikin sabbin 'yan uwansa.
Saboda haka da ya shiga Facebook bayan shekara 15, sai ya yi ta mamakin ko wani zai gane sunan. Nan ba da da jimawa ba sai ga amsar.
"Ranar Asabar na sanya sunana, kuma suka gano ni a ranar Lahadi."
"A 1995 mun yi kokarin neman shi," in ji Rene kawun Charles yana sheda wa BBC. "Ba mu gano shi ba amma kuma ba mu manta da shi ba. Da farko mun yi tunanin ya mutu. Mun sanya a cikin tarihi.
"Kwatsam! kamar a mafarki, bayan shekara 18 sai ga shi da ransa."
Lokacin da suka fara haduwa sai Oliver ya ce wa Rene "kana kama da kanenka. Kai ne, babu wata tantama."
Wannan ita ce haduwarsu ta farko bayan shekaru da Rene ya tabbatar cewa dan uwansa na raye.
Shirin ba shi ne kadai hanyar da kungiyar Red Cross da sauran kungiyoyin agaji suka bi a kokarinsu na hada kan iyalai ba. Kungiyoyin sun raba hotuna da jerin sunaye sannan aka rika zagayawa da yara a motoci zuwa kauyuka domin neman 'yan uwansu.
A karshe, shugabar kula da bayanai na kungiyar Red Cross a Kigali, Espèrance Hitimana, ta ce sun yi nasarar sake hada mutane 70,000 da 'yan uwansu.
Aikin bai kare ba.
"Mukan samu mutum biyu zuwa uku a duk wata," in ji ta. "A wasu lokutan akan samu nasara wajen gano 'yan uwansu. A wasu lokutan kuma ba mu samun labari. Ba mu da zabi face mu gaya musu cewa mun yi iya abin da za mu iya."
Shirye-shiryen BBC na rediyo sun ci gaba amma an daina karanta sunayen wadanda suka bace.
Yanzu shirin na tinkaho da shirin "Imvo n'imvano" a cikin mayan shirye-shiryenta wanda yanzu ta mayar zuwa kafafen sadarwa na intanet.
Mugenzi wanda yanzu ke gudanar da BBC Great Lakes Service ya bayyana nasarar da yake ganin an samu a shekara 25 da suka gabata.
"Dandali ne na labarai na gaskiya da adalci da 'yancin kai na tsawon shekaru." in ji shi.
Ya san jama'a na iya tuna yadda ta fara da mutane irinsu Rene wanda yanzu ke rayuwa ba tare da kawunsa a Kigali, a kusa da kanensa. Kuma kamar Mugabo da Tuyishimire da ke zaune a kusa da kawunsu Theogene.
Theogene shi ne ya dunkule hakikanin abun da wadannan shirye-shiryen suka kunsa.
"Ba don BBC ba da sun mutu," in ji shi.