Abuja: Ko babban birnin Najeriya na daga cikin birane mafiya tsaro a duniya?

Nigeria's police chief said: "Abuja remains indisputably one of the safest capital cities in the world." Reality Check says Nigerian crime statistics are described by the UN as "patchy and divergent" with many crimes going unreported. However, even its own statistics show Abuja is not among the world's safest cities.
    • Marubuci, Daga Christopher Giles
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Karuwar satar mutane da aikata miyagun laifuka sun girgiza babban birnin Abuja wanda ake gani a matsayin amintaccen wuri ne a Najeriya mara fama da babbar matsalar tsaro.

A kokarin kawar da fargabar da ake nunawa game da matsalar, shugaban 'yan sandan kasar, Mohammed Adamu, ya ce Abuja na daga cikin wurare mafiya karancin miyagun laifuka a duniya.

Shin maganarsa gaskiya ce?

Kafin mu yi dubi ga alkaluman, yana na kyau mu yi la'akari da sahihancin alkaluman muggan laifuka a kasar.

Kwararru ba su daukarsu da kima sosai. Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta baya-bayan nan kan aikata kisan kai ya nuna akwai bambance-bambance a alkaluman Najeriya.

Kwararru a fannin tsaro sun ce akwai manyan laifuka da dama da ba a kai kararsu a Najeriya saboda rashin yarda da 'yan sanda da rashin jami'an 'yan sandan a inda aka yi laifin da kuma tunanin cewa kai wa jami'an tsaro kara na iya dagula al'amarin.

Kungiyar binciken kimiyya kan aikin dan sanda ta kasa da kasa (IPSA), wadda ta kunshi jami'an tsaro da masana, ta ayyana Najeriya a matsayin koma baya wurin rashin yarda da 'yan sanda da kuma cin hanci da rashawa da rashin tsaro.

Saboda haka akwai yiwuwar alkaluman da hukumomin kasar ke fitarwa ba su bayyana hakikaknin yanayin miyagun laifuka a Abuja da fadin kasar ba.

Bari mu dubi alkaluman da suka samu, ta hanyar fara kwatanta alkaluman kisan kai da aka tattara a Abuja da na wasu manyan biranen duniya.

Global city homicide rates. Deaths per 100,000. *Abuja and Lagos figures are murder rates, which don't include non-intentional killing. .

Bisa wannan alkaluma, Abuja ba ta cikin birane mafiya aminci na duniya kamar yadda shugaban 'yan sandan kasar ya yi ikirari. Akwai wasu manyan birane da dama da za a iya kwatantawa da Abujan domin tabbatar da hakan.

Alkaluman da gwamnatin Najeriya ta fitar sun nuna cewa yawan kisan da ake samu a babban birnin kasar ya fi adadin da ake samu a birni mafi girma a kasar wato Legas.

Batun sauran matakan tsaron lafiya fa?

Sashen binciken sirri kan tattalin arziki (EIU) kan wallafa ratoto kan miyagun laifuka a birane 60 ta la'akari da wasu alamu 57.

Rahoton ya ayyana Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a matsayin birni mafi aminci a Nahiyar Afrika da matsayi na 44. Sunan Abuja bai bayyana a rahoton ba, amma Legas ce ta karshe a jerin biranen da ke cikin rahoton.

Babu kokwanto cewa miyagun laifukan da ake aikatawa a Legas sun ninka na Abuja sau uku, kamar yadda alkaluman da gwamnatin Najeriya ta fitar a 2017.

But Lagos is a much bigger city, and remember - the official recorded murder rate per capita was higher for Abuja.

Duk da cewa Legas ta fi Abuja girma, amma yawan kisan kai da ake yi a Abuja ya fi yawa, a cewar rahoton.

Saboda haka amincin da ke Abuja bai kai na Tokyo da Singapore da Osaka da kuma Amsterdam ba, wadanda su ne birane mafiya aminci na duniya.

Nigerian police officers

Asalin hoton, Getty Images

Abuja a tsare take kuma yawancin mazaunanta mawadata ne. An fara gina ta daga tushe ne tun a shekarun 1980 sannan ta zama babban birnin Najeriya a 1991.

A nan fadar gwamnatin kasar take kuma ita ce matattarar ofisohin jakadancin kasashe da hukumomin kasa da kasa da kamfanoni.

Sai dai rigingimun da ke faruwa a sassan kasar da kuma wadatar da ke Abuja, na iya zame wa Abuja barazanar kwararowar miyagun laifuka da rikice-rikice zuwa cikin birnin.

Mazauna garin sun bayyan wa BBC Hausa damuwarsu game da karuwar satar mutane. Sun kuma nuna takaicinsu game da kalaman shugaban na 'yan sandan kasar.

Shugabar kungiyar Bring Back Our Girls, Oby Ezekwesili

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya ta sha fama da matsalolin tsaro a yankin arewa maso gabas. Oby Ezekwesili ita ce shugabar kungiyar Bring Back Our Girls masu fafutukar ganin an dawo da daliban makaratar sakandare da ke garin Chibok da Boko Haram ta sace.

"Yanzu an wayi gari birnin Abuja, wanda a baya ake wa kallon tudun mun tsira daga rikice-rikice a wasu sassa, shi ma yana cikin hadari," in ji Nnamdi Obasi na kungiyar International Crisis Group.

"Kwararowar mutanen da suka yi kaura daga karkara saboda talauci da tashe-tashen hankula da muggan laifuka a sassa da dama na kasar na kara yawan matasa marasa aiki a birnin.

Da yawa daga cikin matasan na fuskantar hadarin fadawa cikin miyagun laifuka," a cewarsa.

Presentational grey line
Reality Check branding
Presentational grey line