Arsenal na shakkar fafatawarta da Watford - Granit Xhaka

Kyaftin din Arsenal, Granit Xhaka ya ce shakkun da 'yan wasan kungiyar suka nuna yayin arangamarsu da Watford na daga cikin abin da ya sanya kungiyar ta samu damar farke kwallayen biyu da aka zura mata.

Farkewar Watford a wasan ya sanya suka yi canjaras, inda aka tashi a wasan da ci 2-2.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya zura kwallo biyu a zagayen farko na wasan a ragar Watford.

Sai dai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Tom Cleverley ya farke ta farko, yayin da Roberto Pereyra ya farke ta biyu a bugun fenariti.

"Babu wanda ya so farkewar da aka yi mana. dab da tashi a wasan muna cikin farin ciki saboda munyi tsammanin za mu yi nasara" In ji Xhaka.

"bamu tabuka rawar gani ba bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, saboda mun sakankance da kuma sanya shakku."

"Ba mu nuna kwarewar wasanmu ba a na biyu, kuma mun kasance masu matukar firgita."

Kwallon farko da Watford ta zurawa Arsenal na zuwa ne bayan sakacin dan wasan bayan kungiyar, Sokratis Papastathopoulos da hakan ya bawa Cleverley farkewa.

Tun daga farkon kakar wasa ta bara 'yan wasan Arsenal sun tafka kura-kurai 14 da hakan ya janyo suka rasa lashe gasar Premier.

Xhaka ya kara da cewa: "Kowacce kungiyar da ke taka leda a Premier tana da karfin da za ta iya zura kwallo, sai dai ya kamata 'yan wasan su kasance cikin nutsuwa, domin hakan ne zai ba su damar tsallakawa matakan da suke so a wurinmu wannan karon hakan ba ta samu ba."

Bayan nasarar da Arsenal ta samu sau biyu a Premier wanda ta samu nasarar casa Newcastle da Burnley, wannan karon ta gaza cimma sakamakon kaye har sau uku da ta sha a hannun Liverpool da Tottenham da kuma wasanta da Watford da shi ma ta sha kashi.

Emery ya ce "Muna da matasan 'yan wasa da dama." Ya kamata mu ba su horo sosai saboda wasan da za su tunkara nan gaba.

"Za mu cigaba da yadda muke gudanar da atisaye. Muna bukatar inganta yadda muke gudanar da shi. Akwai bayanai da ya kamata muyi aiki a kai. Amma wannan wasan ya koya mana izina."