Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 5 da ba ku sani ba game da Mugabe
1) Yana tashi da asuba, yana son abincin gargajiya.
Kafin mutuwarsa, yana tashi da asubahi tsakanin 4:00 zuwa 5:00 domin motsa jiki, makusantansa sun bayyana cewa yana yawan sauraren BBC a rediyo.
Abincin da Mugabe ya fi so shi ne sadza, wani abincin gargajiya na Zimbabwe mai kama da tuwo.
2) Yana matukar kaunar wasan kurket
A lokacin da Mugabe ke shugaban kasar Zimbabwe, yana daga cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar kurket ta kasar.
Fadarsa a lokacin na kusa da wajen wasanni na birnin Harare, wanda hakan ke bashi damar zuwa kallon wasan musamman idan ana gasa.
Marigayi Mugabe ya sha bayyana cewa yana san kowa a Zimbabwe ya iya buga wasan kurket.
3) Ba ya son rashin nasara.
Tun Mugabe na karamin yaro, an shaida cewa ya iya buga wasan tennis.
Amma duk lokacin da yayi rashin nasara, yakan yi wurgi da abin buga wasan tennis din.
An shaida cewa idan yayi rashin nasara yakan sadda kansa kasa ya saukar da kafadunsa ya fita daga wajen wasan ba tare da cewa kowa komai ba.
4) Ya fi son Cliff Richard fiye da Bob Marley
Marigayi Edgar Tekere, wani tsohon dan siyasa a Zimbabwe ya shaida wa BBC cewa Mista Mugabe bai ji dadi sosai ba da aka kira Bob Marley ya yi wasa ranar samun 'yancin kan kasar a 1980.
A wancan lokacin, Mista Mugabe ya fi bukatar shahararren mawakin nan na Birtaniya Cliff Richard domin yayi wasa a wajen bikin samun 'yancin kai na kasar.
Hakazalika yana sha'awar wakokin mawakin nan na Amurka Jim Reeves.
5) Yana yawan yabon Kwame Nkrumah
Mista Mugabe ya fara ra'ayin siyasa tun yana kasar Ghana a lokacin yana malamin makaranta.
Ya je kasar ne shekara daya bayan dan siyasar nan na Ghana kuma dan kishin Afirka Kwame Nkrumah ya kai kasar ga samun 'yancin kai a 1957.
Ghana ce kasa ta farko da ke yamma da sahara da ta fara karya lagon mulkin mallaka.
Mista Mugabe ya ce samun 'yancin da Ghana suka yi ya bashi kwarin guiwa sosai.