Guguwar Dorian: Mutun 5 sun mutu a Bahamas

Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 5 ne suka mutu, yayin da muguwar goguwar nan ta Dorian ke ci gaba da lalata sassan tsibirin Bahamas.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa goguwar nan ta Dorian ka iya ci gaba da tafka barna a tsibirin Bahamas nan da wasu awanni masu zuwa.
Firai ministan kasar Hubert Minnis ya ce an tabbatar da mace-macen ne a tsibirin Abaco, wanda ya fi jigata daga barnar goguwar.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce gidaje kimanin 13,000 ake tsammanin sun lalace ya zuwa yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Minnis ya ce har yanzu wannan goguwa ta Dorian na da matukar hadari.
Hotuna sun nuna yadda ruwan da ya yi ambaliya ke kara tudadowa, yana wancakali da motoci da watsi da itatuwa.
Hotunan bidiyon mazauna yankunan da abin ya shafa da kuma rahotannin da ke fitowa sun nuna yadda ambaliya ta mamaye kusan ko ina, inda wasu mutane ke hawa rufin gidajensu domin gudun kada ruwa ya shanye su.

Asalin hoton, Getty Images
Dorian dai ita ce goguwa mafi karfi da ta fada wa tsibirin na Bahamas, sannan masana yanayi na sa ran za ta matsa zuwa gabar Amurka na gabaci.











