Hotunan barnar da mahaukaciyar guguwa ta yi a Mozambique

Mahaukaciyar Guguwa ta Cyclone Idai a yankin Kudancin Afirka ta dai-daita dubban mutane a cewar Majalisar Dinkin Duniya, inda ambaliyar ruwa da tashin hankali ya shafi kasashen Mozambique da Zimbabwe da Malawi.

Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tabo ya cika cikin wani gida a garin Chimanimani na kasar Zimbabwe
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna unguwar Buzi a tsakiyar Mozambique sun hau kan rufin gidajensu bayan wucewar guguwar Idai
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata bishiya ta fado cikin wani gida da guguwar ta lalata
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata tsohuwa tana rawar sanyi a gaban gidanta bayan wucewar guguwar a birnin Beira
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutanen da suka rasa gidajensu na cin abincin da aka raba masu bayan isa filin jirgin sama a birnin Beira da ke gefen ruwa a tsakiya Mozambique ranar Laraba
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya na raka mutanen da suka rasa gidajensu zuwa inda za su zauna a birnin Beira
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata da aka dauka akan gadon marasa lafiya bayan da aka dauko a jirgi mai saukar ungulu a garin Chimanimani
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Guguwar ta lalata igiyoyin wuta da dama a titunan birnin Beira
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jane Chitsuro mai shekarar 42 wacce ta tsira daga guguwar a kan gadon asibiti a gabashin Zimbabwe
Mozambique Cyclone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojoji na taimaka wa mutanen da guguwar ta afkawa gidajensu zakulo wasu kayansu daga cikin turbaya