Rouhani: Ba mu amince mu tattauna da Amurka ba

Hassaan Rouhani na Iran

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Hassaan Rouhani na Iran

Kwana daya bayan taron G7, shugaban Iran ya yi fatali da kalaman Mista Trump cewa Amurka na iya tattaunawa da kasarsa.

Taron da Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya dauki nauyinsa, taron da kuma aka kammala da karfin gwuiwar samar da mafita kan batutuwa masu sarkakiya.

Amma da alama ba a kwana biyu ba ma, sai ga shugaban Iran ya na fatali da tayin Mista Trump da ke cewa Amurka na son tattaunawa da kasarsa idan yanayi ya samar da haka.

Shugaban ya ce Iran ba za ta zauna bisa teburin tattaunawa ba sai bayan Amurka ta janye jerin takunkumin da ta kakaba ma ta.

A ranar Litinin, Shugaba Trump ya yi wani shagube na yiwuwar bai wa Iran wani sassauci a bangaren kasuwanci da cinikayya - har ma ya tabo batun ba ta damar karban bashi.

Abin da ya fito fili shi ne dole kasashen biyu - Amurka da Iran su kaucewa kara fadawa cikin wani sabon rikici.

Kuma abu muhimmi shi ne shugabannin kasashen biyu su amince da wani mataki da za su iya nunawa 'yan kasashensu a matsayin wata nasara komai kankantar ta.