Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matan da aka yi safarar su na cikin wahala a Najeriya - HRW
Kungiyar Kare Hkkin Bil'adama ta Human Rights Watch, HRW, ta ce har yanzu da dama daga cikin matan da aka mayar da su zuwa Najeriya, bayan sun fuskanci matasalolin rayuwa sakamakon safarar su da aka yi zuwa wasu kasashe, na fama da matsaloli da suka hada da talauci da rashin lafiya da kuma mummunan yanayi.
A wani sabon rahoto da ta saki ranar Talatar nan, kungiyar ta ce maimakon hukumomin Najeriya su sama wa matan tallafin da ya kamata domin sake inganta rayuwarsu, sun sake jefa rayuwarsu cikin halin ha'ula'i ta hanyar sake tsare su ba bisa ka'ida ba.
Rahoton na HRW mai shafi 90 wanda yake da taken, "' Za ki yi fatan mutuwa': Safarar mata da 'yan mata a Najeriya," na kunshe da bayanai dangane da yadda hakikanin safarar mata take gudana a Najeriya.
Kungiyar ta Human Rights ta ce ta bankado irin yadda mata da 'yan matan da aka yi safarar su zuwa wata kasar da ke son koma wa gida, ke shiga cikin halin tsaka mai wuya, inda ta ce hukumomin Najeriya na tsare su.
Mai bincike a Kungiyar ta HRW, Agnes Odhiambo, ta ce, " Mun kadu sosai kan yadda muka samu mata da 'yan matan da aka yi safarar su a kulle a wasu wurare na gwamnati ba tare da samun damar zanta wa da iyalansu ba har tsawon watanni masu dama."
Human Rights Watch ta ce ta tattauna da mata da 'yan mata 76 da aka yi safarar su, da jami'an gwamnati da shugabannin kungiyoyin farar hula da cibiyoyin da ke ba da tallafi ga shirin dakile safarar mata da 'yan mata a Najeriya.
Yawaitar safarar mata da 'yan mata zuwa kasashen Turai da ma kasar Libya ya janyo kafafen yada labarai tattauna batun da manufar sanya Najeriyar daukar matakai.
Da dama daga cikin matan da 'yan matan da aka ceto zuwa Najeriya bayan an yi safarar tasu na kasancewa a yanayi irin na kangin bauta a Najeriyar.
Hukumomi a Najeriyar dai sun dauki matakai da dama na inganta rayuwar mutanen da aka yi safara da su ta hanyar kafa musu sansani da kula da lafiyarsu da sama musu ayyukan yi da kuma ba su tallafi domin gudanar da rayuwarsu kamar ta kowace 'ya mace.
To sai dai kungiyar ta ce bai kamata hukumomin Najeriya sun sa wadanda aka yi safarar a cikin kangin da zai iya tilas musu kwammacewa rayauwar da suka baro ba.