Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta ceto yara 10 daga masu safarar mutane zuwa Rasha
Hukumomi a Najeriya sun ce sun dakile wasu masu safarar mutane tare da ceto yara 10 wadanda ake son kai wa Moscow da sunan zuwa kallon gasar kofin duniya.
Gwamnatin Najeriyar ta yi gargadin cewar masu laifi suna amfani da gasar cin kofin duniya domin samun takardar shiga ga yara kanana wadanda masu safarar mutane za su yi amfani da su ta hnayar da bai dace ba.
Yara mata tara da kuma yaro namiji daya suna dab da shiga jirgin sama na kamfanin jiragen sama na Turkiyya ne daga Legas zuwa Moscow, a lokacin da jami'an hukumar da ke yaki da fataucin mutane (NAPTIP) su ka ceto su.
An kama mutum biyar da ake zargi, ciki har da dan sanda daya da kuma wani jami'in wajen fitar da yaran.
An bai wa yaran fasfo da kuma takardar shaida na masu goyon bayan 'yan kwallo a filin jirgin, domin a dauke su tamkar masoya kwallon kafa ne masu son tafiya Rasha kallon gasar kwallon kafar ta duniya.
Mai yiwuwa ne bayan sun kai isa kasar, za a kai su wasu kasashen daban inda masu safarar mutanen ke da abokai wadanda za su tilasta musu yin aiki.