Me ake cewa game da sabbin ministocin Buhari?

A ranar Laraba ne shugaba Buhari ya rantsar da sabbin ministoci

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da ake ci gaba da tsokaci kan sabbin ministoci 43 da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar a ranar Laraba, PDP ta ce shugaban ya rage masu mukami.

Babbar jam'iyyar adawar ta soki sabon zubin gwamnatin jam'iyyar APC mulki, inda ta bayyana shakku cewa da wuya ta iya kawo karshe matsalolin da Najeriya ke fuskanta da wannan zubin ministocin.

PDP ta bayyana cewa irin mutanen da aka nada ministocin da kuma irin yadda aka raba masu ma'aikatu da za su jagoranta, wata alama ce cewa "da wuya gwamnatin ta iya magance matsalolin da kasar ke fuskanta."

Sakataren jam'iyyar ta PDP na kasa, Sanata Umaru Tsauri, ya ce "kamar Shugaba Buhari bai san matsayinsa ba saboda ya rage wa ministoci mukami kwarai da gaske."

"Shugaban kasa ya ce duk wanda ke bukatar wani abu daga gare shi, to ya bi ta hannun shugaban ma'aikatar fadarsa," in ji Sanata Tsauri.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar:

Bayanan sautiTattaunawarmu da Sanata Umaru Tsauri

A ranar Laraba ne Shugaban ya rantsar da ministoci 43, karin guda bakwai kenan kan wadanda ya bai wa mukamai a zangon mulkinsa na farko.

Ministocin da mukamansu

1- Uchechukwu Ogah (Abia) - Ministan Ma'aikatar Tama da Karafa

2- Muhammad Musa Bello (Adamawa) - Ministan Abuja

3- Godswill Akpabio (Akwa Ibom) - Ministan Neja Delta

4- Chris Ngige (Anambra) - Ministan Kwadago

5- Sharon Ikeazor (Anambra) - Karamar Ministan Muhalli

6- Adamu Adamu (Bauchi) - Ministan Ilimi

7- Mariam Katagum (Bauchi) - Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari

8- Timipre Sylva (Bayelsa) - Karamin Ministan Man Fetur

9- George Akume (Benue) - Ministan Ayyuka Na Musamman da Harkokin Kasashen Waje

10- Mustapha Baba Shehuri (Borno) - Karamin Ministan Noma da Raya Karkara

11- Goddy Jedi Agba (Cross River) - Karamin Ministan Lantarki

12- Festus Keyamo (Delta) - Karamin Ministan Neja Delta

13- Ogbonnaya Onu (Ebonyi) - Ministan Kimiyya da Fasaha

14- Osagie Ehanire (Edo) - Ministan Lafiya

15- Clement Anade Agba (Edo) - Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare

16- Otunba Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti) - Ministan Masana'antu da Zuba Jari

17- Geofery Onyeama (Enugu) - Ministan Harkokin Kasashen Waje

18- Ali Isa Ibrahim Pantami (Gombe) - Ministan Sadarwa

19- Emeka Nwajiuba (Imo) - Karamin Ministan Ilimi

20- Suleiman Adamu (Jigawa) - Ministan Albarkatun Ruwa

21- Zainab Shamsuna Ahmed (Kaduna) - Ministar Kudi

22- Mohammed Mahmoud (Kaduna) - Ministan Muhalli

23- Sabo Nanono (Kano) - Ministan Harkokin Noma

24- Bashir Magashi (Kano) - Ministan Tsaro

25- Hadi Sirika (Katsina) - Ministan Sufurin Jiragen Sama

26- Abubakar Malami (Kebbi) - Ministan Shari'a

27- Ramatu Tijani (Kogi) - Karamar Ministar Abuja

28- Lai Mohammed (Kwara) - Ministan Yada Labarai da Al'adu

29- Gbemisola Saraki (Kwara) - Karamar Ministar Sufuri

30- Babatunde Raji Fashola (Lagos) - Ministan Ayyuka da Gidaje

31- Adeleke Mamora (Lagos) - Karamin Ministan Lafiya

32- Mohammed H. Abdullahi (Nasarawa) - Karamin Ministan Kimiyya da Fasaha

33- Zubairu Dada (Niger) - Karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje

34- Olamilekan Adegbiti (Ogun) - Ministan Ma'adanai da Karafa

35- Tayo Alasoadura (Ondo) - Karamin Ministan Kwadago

36- Rauf Aregbesola (Osun) - Ministan Harkokin Cikin Gida

37- Sunday Dare (Oyo) - Ministan Matasa da Wasanni

38- Pauline Tallen (Plateau) - Ministar Harkokin Mata

39- Rotimi Amaechi (Rivers) - Ministan Sufuri

40- Mohammed Maigari Dingyadi (Sokoto) - Ministan Harkokin 'Yan Sanda

41- Saleh Mamman (Taraba) - Ministan Lantarki

42- Abubakar B. Aliyu (Yobe) - Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje

43- Sadiya Umar Faruk (Zamfara) - Ministar Jin-kai da Walwalar 'Yan kasa