Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rumbun makamai na uku ya fashe a Bagadaza
An kara samun fashewar makamai a wani sansanin da ake adana makamai mallakin wata kungiyar mayaka 'yan Shi'a da Iran ke mara wa baya.
Ba a dai san dalilin fashwar makaman ba, wanda kuma shi ne irinsa na uku a cikin wata guda a wuraren adana makamai mallakin kungiyar ta 'yan Shi'a.
Wasu na ganin Amurka da Isra'ila ne ke da alhakin aukuwar lamarin.
Bakin hayaki ya sake turnuke wani yanki na birnin Baghdad, amma a wannan karon a wani sansanin sojoji ne da ke karkashin ikon wata kungiyar 'yan Shi'a da suka taimaka wajen fatatakar kungiyar IS daga kasar.
A makon jiya irin wannan fashewar ta auku a wani sansanin sojojin da ke Bagadazan, lamarin da ya janyo rokoi na tarwatsewa suna fadawa sassan birnin.
A wancan karon an dora laifin fashewar bama-baman kan matsanancin zafi ne da rashin adana makaman kamar yadda ya kamata.
Kuma gwamanti ta umarci da a tashi dukkan depo-depo na makamai zuwa wasu yankunan kasar daga Bagadaza.
Amma yadda fashewar ke aukuwa a wasu sansanonin da Iran ke da mabiya ya janyo ana rade-radin cewa Amurka da Isra'ila ne ke da hannu - saboda gargadin da ta yi wa Iran a baya cewa za ta yi amfani da wasu hanyoyin dakile karfin fada ajin da Iran din ke da shi a yankin.