Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakin Donald Trump na sa ido kan Iran ya fusata Iraq
Gwamnatin Iraki ta bayyana rashin jin dadinta game da shawarar da Shugaba Trump na Amurka ya yanke na jibge wasu sojojin Amurkar a kasar domin sa ido kan Iran.
Shugaban Iraki Barham Salih ya ce Mista Trump bai nemi amincewar kasarsa ba kafin ya dauki wannan matakin.
Ya kuma bayyana shawarar ta Amurkar a matsayin "mai daure kai" saboda yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla ita ce ta dakarun Amurka su tallafa wa na Iraki fatattakar 'yan ta'adda daga kasar.
Kalaman Shugaban Amurka Donald Trump game da kasancewar dakarun Amurka a Iraki sun tayar da hankula. Shugaba Salih ya ce ba zai bari a yi amfani da kasarsa wajen kai wa makwabtanta hari ba.
A karshen makon jiya Donald Trump ya ce sojoji 2,000 za su isa wani sansanin sojin Amurka da ke lardin Anbar daga Syria kwanan nan. Ya kuma ce babban aikin wadannan sojjin shi ne na sa ido a kan Iran.
Tabbas gwamnatin Iraki ba za ta amince da wannan matakin na Amurka ba, ganin cewa gwamnatin na da goyon bayan kasar ta Iran.
Akwai kuma batun tattaunawar da ake yi game da cigaba da zaman da ita kanta Amurkar ke yi a cikin Iran. Amma wannan matakin da Mista trump ke son dauka ba zai haifar da da mai ido ba ga ita kanta Amurkar da ma Iraki.
A maimakon haka, matakin na iya zaburad da jami'an gwamnatin Irakin su nemi Amurka ta tattara inata-inata ta bar kasar baki daya.