Za mu tsage gaskiya a ayyukan NNPC - Kyari

Asalin hoton, OTHERS
Sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya ya ce kamfanin na shirin hada guiwa da wata sabuwar matatar man fetur mai zaman kanta da ake ginawa a jihar Lagos, domin mayar da kasar ta zamo mai samar da mai ga kasashen yankin.
Makasudin wannan yunkuri na hada guiwa da matatar man fetur din ta Dangote, wadda za ta rinka tace mai da ya kai ganga 650,000 a kowace rana, na daga cikin sabbin tsare-tsaren shugaban kamfanin Mele Kolo Kyari na yin garambawul ga kamfanin na NNPC ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa na duniya.
Matatar man fetur din da attajirin nan Aliko Dangote ke samarwa za ta zama wadda ta fi kowace girma a Afirka.
Kyari, wanda ke kokarin kara tabbatar da gaskiya a al'amuran kamfanin, ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa NNPC na so ya zama na farko da zai rinka samar wa matatar man ta Dangote da danyen mai.
Ya ce yarjejiniyar "wata kwantaragi ce ta samar da danyen man fetur."
Kyari, wanda aka nada a mukamin cikin watan Yuli, ya ce zai wallafa sunayen wadanda ke gudanar da kwangilar danyen man fetur ta kasar, da kuma kamfanonin da suka yi nasara wurin samun aikin musayar danyen mai na Najeriya da tace shi.
Har ila yau ya ce zai bayyana rahoton asusun kamfanin wanda aka tantance.
Ya ce bayyana ayyukan kamfanin da kuma shirin bunkasa harkar cinikayyar man fetur na kasar zai bunkasa zuba jari, wanda a baya ya gurgunce saboda rashin tabbas da rashin gaskiya.
An dai kwashe shekaru ba a wallafa bayanan irin wadannan kwangiloli ba, kuma a cikin shekaru da dama ana yi wa kamfanin kallon wanda ke cike da ayyukan rashawa, lamarin da ya sha musantawa.
Kamfanin na NNPC na kuma kokarin ganin ya farfado da matatun man fetur na gwamnati, duk da cewa matatar mai ta Dangote za ta iya tace man da ya zarce abin da Najeriyar ke bukata.
Kyari ya ce akwai bukatar farfado da matatun, inda ya ce Najeriya za ta iya zamowa mai samar da mai ga nahiyar Afirka.











