#RevolutionNow: Kama Sowore take hakkinsa ne - HRW

Kungiyar ta Human Rights Watch, ta yi Allah-wadai da kama Omoyele Sowore mai jaridar Sahara Reporters ta intanet wanda kuma shi ne madugun gangamin #RevolutionNow da ke kokarin matsa wa gwamnatin Najeriya lamba wajen 'sauya' halayyarta.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, mai bincike ga kungiyar, Anietie Ewang, ta ce "Idan dai har an tsare Omoyele Sowore ne da manufar taka wa zanga-zangar da ya shirya burki, hakan na nuna irin rashin hakurin gwamnati ga masu suka, a fili."
Ta kara da cewa "Yin amfani da kalmar sauyi ta 'revolution' a matsayin wani take ba zai sa gwamnati ta ayyana hakan a matsayin ta'addanci ba sannan bai kamata a kalle shi a matsayin laifi ba."
Daga karshe, Anietie Ewang ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta " kawo karshen cin zarafi da tursasa da kuma tsorata mutane da ma kungiyoyin da suke yi wa gwamnati suka mai ma'ana dangane da ayyukanta da tsare-tsarenta, ciki har da kungiyar Amnesty International."
"Dole ne ko dai a saki Sowore da sauran mutanen da ake tsare da su ba tare da wani sharadi ba ko kuma a gurfanar da su gaban kuliya a cikin sa'o'i 48." In ji Anietie Ewang.
Sai dai hukumar farin kaya ta DSS ta ce tun ranar Litinin ta gurfanar da Sowore a gaban kuliya.
A ranar Asabar ne dai jami'an tsaro na farin kaya wato DSS suka kama Sowore bisa zargin "yunkurin tayar da tarzoma" a Najeriya.
Sai dai duk da haka abokan Omoyele Sowore sun gudanar da jerin zanga-zangar a wasu biranen Najeriya da suka hada da Legas da Abuja da Fatakwal.
Za a iya cewa zangar-zangar ta neman "juyin juya-hali" da aka gudanar ba ta yi tasiri ba ko kadan a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Kano da Kaduna da jihar Neja.
Masu sharhi dai na ganin rashin tagomashin zanga-zangar a arewacin kasar ba ya rasa nasaba da farin jinin da Shugaba Muhammadu Buhari yake da shi ba a yankin.













