Yadda ake tantance kura-kurai a Qur'ani a Saudiyya

Saudiyya

Asalin hoton, Saudi gazette

Bayanan hoto, A kullum ana fito da kwafin Kur'anin da ake kai wa Saudiyya domin duba kura-kurai

A kullum ta Allah a kan fito da kusan kwafin kur'ani dubu tara daga masallacin Makka domin gyaran kura-kuran da suke ciki walau dai kuskuren baki ko kuma rashin cikar shafuka kamar yadda darakatan da ke kula da littafan masallatai masu tsarki, Khaled Al-Harithy ya shaida wa jaridar Saudi Gazette.

Khaled Al-Harithy ya ce Alhazan kasar Syria ne ke kai mafi yawancin Kur'anan da ke dauke da kura-kuran baki da manufar neman samun lada a wurin Allah.

Ya kara da cewa ma'aikata 70 zuwa 140 ne ke aiki ba dare ba rana wajen tantance sahihancin Kur'anan.

"Fadar shugaban kasa ta samar da fiye da kwafin Qur'ani miliyan daya da aka buga a madaba'ar Sarki Fahd da ke Madina wadanda kuma aka sanya a msallacin na Makka." In ji Alharithy.

Alharithy ya kara haske kan yadda ake tsaftace kantoci kimanin dubu uku na Kur'anai a masallacin na Makka.

Ya kuma ce a lokacin watan Ramadana da na aikin hajji suna karbar katan-katan din kur'ani guda 100 a kullum, inda a kowane katan a kwai kwafin kur'anin 80 zuwa 90.

Daga karshe Alharithy ya ce a kullum suna raba kwafin kur'ani 1000 ga mahajjata tare da dardumar sallah guda daya ga kowane mahajjaci.