Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe Buhari zai bai wa ministoci ofisoshi domin fara aiki?
'Yan Najeriya da dama sun ta zumudi da hasashen cewa a ranar Larabar nan ne Shugaba Buhari zai bayyana ma'aikatun da ministocin da majalisar dattawa ta tantance za su yi aiki a ciki.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai ya yaba wa majalisar dattawa bisa yadda suka gaggauta tantance sunayen ministocin da ya aike masu makon da ya gabata.
'Yan majalisar dokokin dai sun kammala tantance ministocin guda 43 a cikin kwanaki biyar wato daga ranar Larabar makon da ya gabata zuwa Talatar wannan makon.
Majalisar dattawan ta dage tafiya hutunta na shekara da ya kamata ta fara a ranar Alhamis din da ta gabata.
A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce yana fatan kafa majalisar zartarwa nan ba da jimawa ba wato hakan na nufin rarraba ma'aikatu ga ministocin.
Ya ce: "Na gamsu da yadda majalisar dattawa ta amince da ministocin da na aike mata ta yadda suka gaggauta aikin tantancewar"
"'Yan Najeriya na son ganin sakamako kuma da wadannan sunayen ministocin muna da karfin gwiwa cewa za mu fitar da jaki daga duma. Zan bai wa kowane minista daga ciki ma'aikatar da zai yi aiki bayan rantsar da su yayin zaman majalisar zartarwa."
A ranar Larabar nan ne ake sa ran Shugaba Buharin zai sanar da ma'aikatu ga ministoci a yayin zaman majalisar zartarwa da aka saba yi duk Laraba.
Daga cikin ministocin da aka tantance dai guda 43 bakwai ne mata, inda 12 daga cikinsu suka samu damar dawowa.
Jerin sunayen ministoci
1. Chris Ngige
2. Hadi Sirika
3. Rotimi Amaechi
4. Festus Keyamo
5. Uche Ogah
6. Emeka Nwajuiba
7. Sadiya Farouk
8. Musa Bello
9. Babatunde Fashola
10. Godswill Akpabio
11. Sharon Ikeazor
12. Ogbonnaya Onu
13. Akpa Udo
14. Adebayo (Ekiti)
15. Timipre Sylva
16. Osagie Ehimere
17. Lai Mohammed
18. Baba Shehuri (Borno)
19. Isa Pantami
20. Gbemi Saraki
21. Ramatu Tijani
22. Clement Abam
23. George Akume
24. Sunday Dare
25. Geofrey Onyeama
26. Tayo Alasaodura
27. Olorunminbe Mamora
28. Mohammed Abdullahi
29. Adamu Adamu
30. Maryam Katagun
31. Zainab Ahmed
32. Sabo Nano
33. Zubair Dada
34. Paullen Tallen
35. Abubakar Aliyu
36. Sale Mamman
37. Abubakar Malami
38. Muhammed Mamood
39. Mohammed Adamu
40. Rauf Aregbesola
41. Mustapha Buba Jedi Agba
42. Olamilekan Adegbite
43. Mohammed Dangyadi
Sunayen tsaffin ministoci 12 da suka dawo
- Hadi Sirika
- Chris Ngige
- Rotimi Amaechi
- Babatunde Fashola
- Ogbonnaya Onu
- Lai Mohammed
- Adamu Adamu
- Geofrey Onyema
- Zainab Ahmed
- Osagie Ehimere
- Abubakar Malami
- Baba Shehuri