Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sunayen Ministoci: Shirme kawai 'Buhari yake yi'
Babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya PDP, ta ce babu wani abin birgewa a game da jerin sunayen mutanen da shugaban kasar ya fitar domin nada su ministoci, hasalima "shirme da bata lokaci" kawai ya yi.
A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, PDPn ta ce jerin sunayen da Shugaba Muhammadu Buharin ya mika wa Majalisar Dattawa, ranar Talata, domin amincewa, ba shi da wani armashi ko alamu na samar da kyakkyawan shugabanci a karkashin jam'iyyar APC.
Jam'iyyar ta ce abin haushi ga 'yan Najeriya, takardar cike take da sunayen mutanen da ba su cancanta ba, wadanda suka kasa tabuka komai kuma suka bar ma'aikatun da suka yi wa minista a baya a watse.
Jerin sunayen 43 sun nuna cewa Buhari, wanda ya kayar da dan takarar PDP Atiku Abubakar a zaben watan Fabrairu, ya dawo da ministoci 13 sannan ya yi watsi da 18, inda kuma ya nada sabbi guda 30. Bakwai daga cikin sunayen mata ne, ciki kuma har da tsaffin gwamnoni bakwai.
A ranar Laraba ne kuma ake sa ran majalisar dattawa za ta fara tantance su kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Sai dai PDP, wacce yanzu haka ke kalubalantar nasarar Buhari a gaban kotun sauraran kararrakin zabe, ta ce takardar jerin sunayen ta nuna lalle ta fito ne daga shugabancin da ba shi da halarcin jama'a.
Bugu da kari bata lokaci kawai aka yi tsawon lokacin da aka dauka ba a fitar da shi ba, kuma ba zai biya bukatu da cimma fatan 'yan Najeriya ba.
Jam'iyyar ta hammayya ta kara da cewa sunayen sun kara nunawa karara gazawa da halin ko-in-kula na Shugaba Buhari da APC kan yadda suka rena 'yan Najeriya, da kuma cewa ba wata alama da suke da ita ta fata da burin bunkasa kasar.
Sanarwar ta kara da cewa sake dawo da wasu tsoffin ministoci wadanda suka gaza, ya nuna Buhari da jam'iyyar APC ba su bar kowa cikin duhu ba cewa ba su da wani buri na fitar da kasar daga matsalar tattalin arziki da ta tsaro, da suka kara jefa kasar ciki a shekara hudu da ta wuce.
Ta ce a halin da kasar ke ciki, da shugabanci ne da ya san abin da ya kamata, to da sai ya tuntubi bangarori da jama'a da dama kafin ya kai ga fitar da sunayen ministocin.
PDPn ta ce idan da Shugaba Buhari da APC suna nufin 'yan Najeriya da alheri da kuma burin farfado da muhimman bangarorin ci-gaba na kasar, da ba za su fito da sunayen wadanda suka taimaka wajen boye dimbin almundahanar da aka yi a gwamnatin Buharin ba a shekara hudun da ta wuce ba.
Haka kuma jerin sunayen da ba zai hada da wadanda za su taimaka wajen mika kudi ga mutane da kungiyoyin da AP ta yi amfani da su ba wajen yin magudi a zaben shugaban kasar na 2019 ba.
Jam'iyyar ta hamayya ta kuma nuna takaici da mamakin yadda jerin sunayen bai kunshi matasa ba, wadanda ta ce su ne manyan gobe ba.
A karshe jam'iyyar ta PDP ta ce, sakamakon wannan koma-baya, a fili take cewa, hanya daya kawai da kasar za ta fito daga matsalar tattalin arziki da tsaro da take ciki a yanzu, ita ce ta kwato nasarar da ta ce dan takararta Atiku Abubakar ya yi, wadda aka kwace, daga kotu.
Ta ce wannan ita ce hanyar da 'yan Najeriyar za su amfana da samun jerin mutanen da suke kwararru kuma masu kishin kasa a matsayin ministoci, wadanda za su ciyar da kasar gaba.
Sunayen sababbin ministoci a karon farko
- Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe
- Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom
- Alhaji Sabo Nanono - Kano
- Gbemi Saraki (Kanwar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki) - Kwara
- Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun
- George Akume - tsohon gwamnan - Benue
- Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa
- Sadiya Farouk - Zamfara
- Maryam Katagum - Bauchi
- Ramatu Tijjani - Kogi
- Sanata Olorunnibe Mamora - Legas
- Sunday Dare - Oyo
- Festus Keyamo - Delta
- Sharon Ikeazor - Anambra
- Sanata Tayo Alasoadura - Ondo
- Pauline Tallen - Filato
- Mustapha Buba Jedi Agba -
- Olamilekan Adegbite - Ogun
- Mohammed Dangyadi - Sokoto
- Abubakar Aliyu - Yobe
- Sale Mamman - Taraba
- Muhammed Mamood - Kaduna
- Uce Ogar - Abia
- Emeka Nwajuiba - Imo
- Akpa Udo
- Clement Abam
- Zubair Dada
- Adeniyi Adebayo - Ekiti
- Mohammed Abdullahi
- Osagie Ehenere
- Bashir Salihi Magashi - Kano
Tsoffin ministocin da suka dawo
- Babatunde Fashola - Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje
- Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri
- Ogbonnaya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha
- Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi
- Sanata Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago H
- Hadi Sirika - Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama
- Zainab Ahmad - Tsohuwar Ministar Kudi
- Lai Mohammed - Tsohon Ministan Watsa Labarai
- Musa Bello - Tsohon Minsitan Abuja
- Abubakar Malami - Tsohon Ministan Shari'a
- Sulaiman Adamu - Tsohon ministan ruwa
- Baba Shehuri - Borno