Yadda 'yan Shia da Hindu suke bikin addini tare

Musulmi da mabiya addinin Hindu suna yi wa juna kara wajen gudanar da bikukuwan addinin tare a kasar Pakistan.

Mabiya addinin na Hindu suna taya musulmi 'yan Shi'a bikin ranar Ashura domin juyayin kashe Sayyiduna Husaini jikan manzon Allah SAW.