Kun san matan da ke cikin ministocin Buhari?

Some of di women wey dey Buhari 2019 ministerial list.

Asalin hoton, Other

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sunayen mutum 43 a matsayin ministocinsa ga Majalisar Dattajai don tantancewa a ranar Laraba.

Mata bakwai ne kacal suka samu shiga jerin.

A yayin da wasu mutanen ke yabonsa kan yawan matan da ke jerin, wasu kuwa suka suke kan cewa yawan ya ragu.

Ko su waye wadannan mata?

Grey line wey dey

Wadannan mata dai da suka shiga jerin ministoci gogaggu ne a fannoni daban-daban kamar bangaren harkar kudi da gwamnati da ma Majalisar Dinkin Duniya.

Sannan kuma masu ilimi ne a fannoni daban-daban.

Zainab Ahmed - (Kaduna)

Zainab Ahmed

Asalin hoton, Twitter/ Zainab Ahmed

Grey line wey dey

Zainab Ahmed ce tsohuwar ministar kudi a karo na farko na mulkin Shugaba Buhari na 2015, inda aka nada ta a watan Satumbar 2018 bayan da Kemi Adeosun ta yi murabus.

Zainab tana da digiri a karatun Akanta da digiri na biyu a Gudanar da Harkar Kasuwanci.

A shafinta na Twitter an rubuta cewa tana da kwarewa a fanin mu'amalar kudi ta tsawon shekara 28.

Sharon Ikeazor - (Anambra)

Sharon Ikeazor

Asalin hoton, Facebook/Sharon Ikeazor

Grey line wey dey

Sharon Ikeazor ce shugabar hukumar fanshon ma'aikatan gwamnati (PTAD) wacce Shugaba Buhari ya nada ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

Rahotanni sun ce a shekararta ta farko a ofis, ta gabatar da tsare-tsare da dama da suka kawo sauyi a hukumar ta PTAD.

Tana da digiri a fannin shari'a daga Jami'ar Benin da kuma takardar shaidar kammala makarantar koyon shari'a a 1985.

A shafinta na Twitter an rubuta cewa tana son ci gaban Najeriya da ganin an bai wa mata damarmaki.

Sadiya Farouq (Zamfara)

Sadiya Farouq

Asalin hoton, Twitter/ Sadiya Farouq

Grey line wey dey

Sadiya Farouq ita ce shugabar hukumar 'yan ci-rani da 'yan gudun hijira.

Tana da digiri a Gudanar da Harkar Kasuwanci daga Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a jihar Kaduna da kuma digiri na biyu a harkokin kasasehn waje da diflomasiyya duk daga wannan jami'ar.

Ambasada Maryam Yalwaji Katagum (Bauchi)

Mariam Y. Katagum

Asalin hoton, UNESCO

Grey line wey dey

Maryam Yalwaji Katagum ita ce Jakadiyar dindindin ta Najeriya a UNESCO tun watan Yunin 2009.

Ta yi digirinta na biyu kan sha'anin mulki da tsare-tsare a Jamiar Legas, sai digiri na farko inda ta karanta harshen Turanci, ta samu shaidar kammala karatu a fannin Ilimi daga ABU Zaria da shaidar kammala karatu a University College, London.

Gbemi Saraki (Kwara)

Gbemi Saraki

Asalin hoton, Facebook

Grey line wey dey

Gbemi Saraki tsohuwar sanata ce da ta wakilci yankin Kwara ta Tsakiya kuma kanwar tsohon shugaban majalisar dattajai Bukola Saraki ce.

Ta yi digirinta na farko a Jami'ar Sussex da ke Birtaniya inda ta karanci Tattalin arziki.

Ramatu Tijani (Kogi)

Ramatu Tijani

Asalin hoton, Twitter/ @HajiaSupporters

Grey line wey dey

Ramatu Tijani ita ce tsohuwar shugabar ata ta jam'iyyar APC ta kasa.

A wata hira da ta taba yi da Jaridar Nation a 2018, ta ce ta halarci Jami'ar Ahmadu Bello Zaria inda ta karanci fannin Tsara birane.

Ta yi digiri na biyu a Sha'anin Mulki. A lokacin ta kara da cewa tana karatun digirin digirgir dinta a fannin Tsaro a wannan ABU din.

Pauline Tallen - (Plateau)

Pauline Tallen

Asalin hoton, Facebook

Grey line wey dey

Pauline Tallen tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar Filato ne a 2007 kuma mace ta farko da ta rike wannan mukamin a arewacin Najeriya.

A shekarar 1999 ta zamo Ministar Kimiyya da Fasaha a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Ta kuma taba yin takarar zama gwamnar Filato a 2011 amma sai Jonah Jang ya kayar da ita.