Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
COZA: 'Yan sanda sun gayyaci Busola da mijinta kan 'fyade'
Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce ta gayyaci Busola Dakolo da mijinta Timi Dokolo da manufar yin bincike kan zargin 'fyade' da ya shiga tsakaninsu.
Sai dai rundunar, a wata sanarwa sa ta wallafa a shafinta na twitter,ta ce gayyatar mutanen ba wai na nufin sammaci ko kuma kamawa a tsare su ba, illa dai gayyata irin ta jin bahasi domin kaddamar da bincike.
Busola Dakolo dai ta fito a wani bidiyo inda ta yi hira da wani dan jarida take sheda masa cewa Fasto Biodun ya yi mata fyade lokacin tana 'yar shekara 16.
Ta kara da cewa ya yi mata fyaden ne fiye da sau daya, inda a karon farko faston ya yi lalata da ita a cikin gidansu da misalin karfe shida na safe.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba ta yi ihu ba domin jama'a su kai mata dauki sai ta ce "Ya rufe min baki."
Busola dai yanzu haka mai dakin fitaccen mawakin nan ce, Timi Dakolo kuma tana da yara.
Fasto ya yi murabus
Tuni dai Fasto Biodun Fatoyinbo ya ce ya dauki matakin ajiye mukaminsa a cocin Commonwealth of Zion Assembly COZA.
A wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin a shafinsa na Instagram, Fasto Biodun, ya ce, ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da jagororin addinin kiristanci na duniya.
A jiya ne dai masu fafutuka suka yi zanga-zanga a Abuja da Legas da manufar bayyana wa mutane irin barnar da wasu fasto-fasto ke yi a majami'u.
Gomman masu zanga-zangar sun ta rera wake-waken yin Alla-wadai da kuma daga kwalaye masu rubutun da ke jan hankalin jama'a da ka da su saki jiki da fasto-fasto dinsu.
An dai gudanar da zanga-zangar ne da manufar nema wa wata wadda ta yi zargin faston cocin Commonwealth of Zion Assembly COZA, Pastor Biodun Fatoyinbo da yi mata fyade.
Masu fafutukar na kara kira ga mata da su fallasa masu irin wannan ta'ada kasancewar zamanin danne hakkin mata ya shude.
To sai dai yayin da masu zanga-zangar suke kokarin goyon bayan Busola Dakolo, a gefe guda an samu wasu masu zanga-zangar da ke goyon bayan Pastor Biodun Fatoyinbo.
Latsa wannan lasifikar ta kasa domin kallon yadda zanga-zangar ta gudana a Abuja