Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kisan Musulmi: Amurka ta dauki mataki kan Myanmar
Amurka ta sanar da sanya takunkumi a kan wasu manyan janar-janar na soji na kasar Myanmar, kan zarginsu da tsabar take hakkin dan adam a kan Musulmi 'yan kabilar Rohingya.
Wadanda takunkumin ya shafa sun hada da babban hafsan ko kwamandan sojin kasar ta Burma, Min Aung Hlaing.
Ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce manyan janar-janar din sojin su hudu su ke da alhakin kisan-gillar da aka aikata a kasar ta Myanmar, a lokacin abin da ya kira kokarin shafe al'ummar Musulmin kasar 'yan Rohingya.
Takunkumin na nufin daga yanzu ba wani daga cikin wadannan hafsoshin soja hudu ko wani daga cikin iyalansu da zai iya zuwa Amurka.
Mista Pompeo ya ce, wannan mataki da Amurka ta dauka shi ne misalin irinsa na farko da wata kasa ta dauka a fili a kan wadannan manyan sojoji na kasar ta Burma.
Ya kuma zargi gwamnatin kasar da laifin kin kama kowa da laifin aikata wannan kisan kiyashi.
Shekara biyu da ta wuce dubban Musulmi 'yan kabilar Rohingya suka rika tserewa zuwa makwabciyar kasar Bangladesh, sakamakon tsattsauran matakin da sojin na Myanmar suka dauka na kisa da gallaza musu.
Su dai 'yan kabilar Rohingya wadanda yawancinsu Musulmi ne, gwamnatin Myanmar na daukarsu a matsayin baki daga Bangladesh, saboda haka ba ta daukarsu a matsayin 'yan kasarta, duk da dadewarsu a kasar, iyaye da kakanni.
A hare-haren, sojojin Myanmar sun ce suna yaki ne da 'yan bindiga na kabilar ta Rohingya, suka musanta cewa suna far ma fararen hula.
Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana matakin sojin a kan mutanen a matsayin wani misali na kokarin share wata kabila daga doron kasa.