Obasanjo: Dole ne Buhari ya daina nuna halin ko-in-kula

Olusegun Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce matsalar tsaro a kasar na iya janyowa a kai wa Fulani harin ramuwar gayya, wanda ka iya jefa kasar cikin tashin hankalin kisan-kare-dangi irin wanda Rwanda ta fuskanta a baya.

A wata wasika da ya rubuta ga Shugaba Muhammadu Buhari, Obasanjo ya yi gargadin cewa "Najeriya na daf da fadawa wani wawakeken rami mai cike da hadari kuma shugaban kasar ne kawai zai iya dakatar da wannan mummunan bala'i".

A shekaru biyun da suka wuce, daruruwan mutane sun mutu a rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da al'ummomi masu noma, musamman a yankin tsakiyar Najeriya.

A baya dai Obasanjo ya sha rubuta wasiku ga shugabanni kuma ya taba rubuta wa Shugaba Buhari ma daf da gudanar da zabukan 2019.

Ana iya cewa dai kisan Funke Olakunrin mai shekaru 58 ne ya tunzura Obasanjo ya rubuta wasikar.

Funke dai 'ya ce ga Reuben Fasoranti, wani mai fada a ji a kabilar Yarabawa.

Shugaba Buhari da rundunar 'yan sandan kasar sun yi Allah-wadai da kisan Misis Olakunrin, kuma shugaban ya sanar da yin garambawul a bangaren tsaro kan manyan tituna a kudancin kasar.

Rundunar 'yan sandan kasar sun ce wasu mutane masu dauke da makamai ne suka kashe ta.

Obasanjo dai ya yi gargadin cewa dole ne Shugaba Buhari ya lalubo hanyoyin wadannan rikice-rikice kabilancin da ke ruruwa a kasar ta hanyar nuna "rashin wariya da halin ko in kula."