Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata ta gano mijinta da ya gudu a hannun dan daudu
Wata mata a Indiya ta hadu da mijinta wanda ya bata tsawon shekara uku, bayan da ta gano shi ta manhajar TikTok.
'Yan sanda sun ce mutumin ya tsere ne a shekarar 2016 kuma tun wancan lokacin yake mu'amala da wani dan daudu.
Wani dan uwar matar ne ya fara gano shi a wani bidiyo tare da dan daudun, al'amarin da ya jawo 'yan sanda fara nemansa.
'Yan sanda sun ce sun bai wa ma'auratayn shawarwari bayan da suka dawo zama tare a yanzu.
Sun gano mijin mai suna Suresh a Hosur - wani birni da ke jihar Tamil Nadu ta kudancin kasar, mai nisan kilomita 200 daga inda matarsa ke zama a yankin Viluppuram.
"Mun tuntubi kungiyar masu sauya halittarsu ta 'yan daudu a gundumar wadanda suka taimaka wajen gano dan daudun a hoton," kamar yadda 'yan sanda suka shaida wa sashen BBC Tamil.
A baya matar da shigar da cigiyar neman mijin nata a wajen 'yan sanda jim kadan bayan guduwarsa - amma ba su iya gano shi ba a wancan lokacin.
TikTok wata manhaja ce da ke bai wa masu amfani da ita damar kirkira da yada bidiyo, kuma manhajar ta shammaci al'ummar Indiya.
Akwai masu amfani da manhajar fiye da miliyan 120 a kasar, amma kuma ana sukar ta saboda sanya wasu abubuwan da ba su dace ba.
A watan Afrilu ne wata kotu a Tamil Nadu ta bayar da umarnin cire manhajar daga kantin sayar da manhajoji na waya kan damuwar da aka nuna na sanya batsa a cikinta.
Amma bayan mako daya aka dage haramcin.