Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tulin shara a Indiya zai wuce ginin Taj Mahal tsawo
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Akwai wani tulin shara a babban birnin Indiya Delhi inda ake zubar da tan 2,000 na shara a kowace rana.
An kiyasta cewa sharar za ta wuce ginin Taj Mahal (mai mita 73) tsawo nan da shekara 2020.
Masu fafutukar kare muhalli sun yi gargadi cewa sharar tana gurbata iska da ruwa wanda zai iya haifar da cutuka mai hadari ga rayuwa.