Mutum miliyan 35 ke fama da matsalar shan miyagun kwayoyi a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin mutum miliyan 35 ne a duniya aka kiyasta cewa ke fama da matsalar miyagun kwayoyi, fiye da yadda aka yi tsammani tun da farko.
An fitar da rahoton ne yayin da a ranar Laraba 26 ga watan Yuni ake bikin ranar yaki da fatauci da miyagun kwayoyi a duniya.
Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ke fama da wannan matsala.
A kwanakin baya Majalisar dokokin kasar ta ce kimanin kwalaben maganin tari mai sinadarin kodin miliyan uku ake shanyewa kullum a jihohin Kano da Jigawa da ke arewacin kasar.
Haka zalika wani bincike da BBC ta yi a bara ya kai ga rufe wasu manyan kamfanonin sarrafa magunguna tare da haramta sayar da maganin tarin mai sinadaran Kodin da Tramadol a kasar.
Tsohon kwamishinan 'yan sanda na jihohin Kano da Katsina Wakili Muhammed ya taimaka wajen yaki da matsala a jihohin, kuma a tattaunawarsu ta musamman da BBC albarkacin ranar ya bayyana irin faman da ya sha da kuma girman matsalar.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirarsa da Habiba Adamu:
Karanta karin labarai masu alaka da wannan












