'Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Sokoto

Rahotanni daga jihar Sakkwaton Najeriya na cewa a kalla mutum 18 ne suka mutu bayan da wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba suka afkawa wani kauye da ke gabashin jihar ranar Litinin da dare.
Wani basarake a yankin ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a kauyen Malafaru da ke yankin karamar hukumar Goronyo.
Harin dai ya zo ne 'yan makonni bayan da wasu 'yan bindigar suka hallaka gwamman mutane a yankin karamar hukumar Rabah ita me da ke gabashin jihar.
Jihar ta Sakkwato dai na da iyaka da jihar Zamfara inda barayin shanu da masu garkuwa da mutane suka hallaka dubban mutane tun daga shekara ta 2011.
Za mu kawo muku karin bayani kan labarin nan ba da jimawa ba.
Batun sata da kisan mutane a arewa maso gabas ya zama ruwan dare musamman a jihar Zamfara mai makwabtaka da Sokoto.
Ko a watan Janairun 2019 nan sai da Rundunar sojin sama ta Najeriya ta tura sojoji da jirgin yaki da makamai zuwa Sokoton domin yaki da 'yan fashi da masu satar mutane.







