Man City za ta dauki dan baya mafi tsada a duniya

Aitor Alcalde

Asalin hoton, Aitor Alcalde

Bayanan hoto, Kungiyoyi sun dade suna rige-rigen daukar Harry Maguire

Harry Maguire mai shekara 26 na kokarin zama dan wasan baya mafi tsada a duniya a makon nan yayin da Manchester City ke shirin daukarsa a kan kudi fan milayan 80 daga Leicester City, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.

Jaridar Marca ta ce Liverpool da Manchester United na rige-rigen daukar dan wasan bayan kasar Sifaniya daga kungiyar Real Betis mai suna Junior Firpo mai shekara 22.

Jaridar TYC Sports ta ruwaito Real Madrid na son daukar Miguel Almiron dan kasar Paraguay daga kungiyar Newcastle.

Kocin Arsenal Unai Emery yana son Arsenal ta fito da kudi domin sayen Wilfried Zaha dan wasan gaban Ivory Coast daga Crystal Palace mai shekara 26, in ji jaridar Sun.

Manchester United za ta rage yarjejeniyar karin wata 12 ta Marcus Rashford yayin da suke shakkar cewa dan wasan mai shekara 21 zai iya barin kulob din idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar badi, in ji Sun.

Har wa yau, Star ta ruwaito cewa an shaida wa Manchester United din cewa sai sun biya fan miliyan 430 idan suna bukatar Raphael Varane na Real Madrid mai shekara 26.

Har yanzu Inter Milan ba su biya fan miliyan 22 ba farashin da Manchester United ta yi wa Romelu Lukaku, mai shekara 26, kamar yadda La Gazzetta dello Sport ta ruwaito.