Amurka ta kai wa Iran 'hari ta intanet

Rahotanni daga Amurka na cewa harin da aka kai ta hanyar intanet ya shafi komfutocin da dakarun juyin-juya halin kasar Iran ke amfani da su wajen sarrafa roka-roka da na'urorin harba makamai masu linzami.

An dai ce an kai harin ne ranar Alhamis, bayan shugaba Donald Trump ya sauya matsayinsa na kai hari kan wasu wurare mallakar Iran.

Ana alakanta harin da martani dangane da harbo jirgi maras matuki mai tsadar gaske mallakar Amurkar da Iran ta yi. Da kuma harin da aka kai wa wasu jiragen ruwa masu dauke da danyen man fetur da Amurka ta dora alhaki kan Iran.

Har yanzu dai babu wata kafa wadda ba ta Amurka ba da ta bayar da yakinin cewa harin da Amurkar ta kai ya lalata kayan yakin Iran din.

Tuni dai Ministan harkokin waje na Birtaniya, Andrew Murrison, ya sauka a Iran, domin tattaunawa kan halin da ake ciki yayin da ake ci-gaba da zaman dar-dar a yankin na Persia.

Ma'aikatar ta ce bulaguron wani bangare ne na matakan tattaunawar diflomasiyya da hukumomin Iran a kan yarjejeniyar 2015 ta shirinsu na nukiliya.

An ce ministan zai yi kokarin yin magana domin ganin Iran din ta dauki matakin gaggawa na yayyafa wa wutar rikicin da ke neman tashi ruwa.

Yanzu haka Amurka ta nemi Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zauna ranar Litinin domin tattaunawa kan Iran.

Shugaba Donald Trump, ya ce shi ba ya fatan gabza yaki da kasar Iran amma kuma ya gargade ta da cewa idan fa har rikici ya barke to fa Amurka za ta gama da ita ne.

Da yake magana da gidan talbijin na NBC a ranar Juma'a, Mista Trump ya kara da cewa a shirye Amurka take domin tattaunawa da kasar Iran.

Sai dai ya nanata cewa babu yadda za a yi Amurkar ta bari kasar Iran ta samar da makaman nukiliya.

Donald Trump ya sake yin karin haske kan sauya tunanin da ya yi na fasa kai wa Iran din hari domin mayar da martani kan harbo jirgin Amurka maras matuki da Iran din ta yi a makon nan, inda ya ce an sanar da shi cewa mutum 150 ka iya mutuwa sakamakon harin.

"Ban so a yi hakan ba. Ba na zaton hakan ya dace," In ji mista Trump.