Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Birtaniya na son Iran ta sassauto domin sulhu
Ministan harkokin waje na Birtaniya Andrew Murrison, ya sauka a Iran, domin tattaunawa kan halin da ake ciki yayin da ake ci-gaba da zaman dar-dar a yankin na Persia.
Ma'aikatar ta ce bulaguron wani bangare ne na matakan tattaunawar diflomasiyya da hukumomin Iran a kan yarjejeniyar 2015 ta shirinsu na nukiliya.
Sanarwar ta kuma ce ministan zai yi kokarin yin magana domin ganin Iran din ta dauki matakin gaggawa na yayyafa wa wutar rikicin da ke neman tashi ruwa.
Ga alama an jima da shirya ziyarar ministan wajen na Birtaniya zuwa Iran, amma kuma ana ganin kasancewarta a wannan lokaci, hakan yana da muhimmanci, bisa la'akari da kallon hadarin-kaji da ake yi wa juna tsakanin Amurka da Iran din a yanzu.
Harbo jirgin sama maras matukin nan na Amurka da Iran ta yi, a wannan yanki na tekun Persia, ya kusa haifar da mummunan dauki-ba-dadi, tsakanin Iran din da Amurka, baya ga harin da Amurkar ta ce Iran ce ta kai kan wasu jiragen ruwa na dakon mai a makon da ya gabata.
A yayin wannan ziyara ta ministan, Birtaniya za ta bayyana damuwarta kan abin da take gani take-taken Iran na neman tayar da zaune-tsaye a yankin.
Ita kuwa Iran za ta matsa wa Birtaniya ne kan ganin ta dauki mataki a kan alkawarin da ta yi mata na samun sassauci kan takunkumin da Amurka ta sanya mata, bayan da gwamnatin Trump ta janye daga yarjejeniyar nukiliya, wadda kasashen Turai har yanzu suke kai.
Ana ganin akwai alamar nan da 'yan kwanaki Iran za ta fara shure wasu daga cikin sharuddan yarjejeniyar, yayin da Amurka ta ce za ta biyo baya da sabbin takunkumi nan da 'yan sa'o'i.
A ranar Asabar, Shugaba Trump, ya ce Iran za ta iya zama babbar kawa ko abokiyarsa, idan har ta amince ta yi watsi da duk wani buri nata na nukiliya.
Amma kuma ya yi barazanar cewa idan a yanayin da ake ciki har aka kai ga rikici, lamarin ba zai yi dadi ba ga Iran ba, zai kawar da ita baki daya.