Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Boko Haram' ta kashe masu kallon kwallon kafa a Najeriya
Masu aikin ceto a Najeriya sun ce a kalla mutum 30 ne suka mutu bayan da aka kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a wani gidan kallo a arewa maso gabashin kasar.
An kuma raunata wasu mutum 40 a harin, wanda aka kai a garin Konduga da ke jihar Borno.
Maharan sun tayar da bama-baman da suke dauke da su ne a wani gida da mutane suka taru domin kallon kwallon kafa a talbijin.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa wata 'yar kunar bakin wake ce ta fara tayar da bam a rumfar mai shayi da misalin karfe 8.30 na dare.
"Hakan ce ta sa mutane suka razana suka gudu, a lokacin ne kuma sai wata 'yar kunar bakin waken ta sake tayar da bam din a bakin kofar gidan kallon kwallon," in ji mutumin wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
"A takaice dai mata uku ne suka tayar da bam din a lokaci guda. Kuma mutane da dama sun mutu, a kalla mun yi jana'izar mutum 17 da safen nan.
"Sannan kungiyar Red Cross ta kwashi mutanen da suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Maiduguri."
Ana kyautata zaton cewa kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, duk da cewa kawo yanzu babu kungiyar ta dauki alhakin kai shi.
Boko Haram ta dade tana kai hare-hare a yankin arewacin Najeriya, inda dubban mutane suka rasa rayukansu, sannan wasu miliyoyi suka rasa gidajensu.
Jami'an tsaro sun nace cewa sun dakile aikace-akacen kungiyar, sai dai har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare musamman na kunar bakin-wake.
Garin na Kodunga ya sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram a baya.
Mutum sama da 20 aka kashe a wani harin kunar bakin-wake a watan Fabrerun 2018.