Daya daga cikin 'yan matan Chibok ta kammala digiri a Amurka

Chibok girls

Asalin hoton, Getty Images

Daya daga cikin 'yan matan sakandiren nan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014 a garin Chibok da ke jihar Borno a Najeriya, ta samu nasarar kammala karatun digiri a wata kwaleji a Amurka.

Dalibar mai suna Palmatah Mutah, mai shekara 23 ta tsere daga hannun 'yan Boko Haram din ne ta hanyar dira daga kan babbar motar da ke tafiya yayin da aka kwashi yan matan daga makarantarsu.

Kammala karantun da ta yi a kwalejin Northern Virginia community na zuwa ne a daidai lokacin da garkuwa da 'yan matan Chibok din ke cika shekara biyar da wata daya da kwana uku.

Palmatah dai ta yi digirin na ta ne a bangaren kimiyya kuma ita ce mace ta farko daga cikin 'yan matan na Chibok da aka yi garkuwa da su da ta kammala digiri kuma dadin dadawa a kasar waje.

A lokacin da aka yi garkuwa da daliban, 'yan Najeriya da dama sun yi ta mamaki kan cewa akasarin 'yan matan kusan 57 da suka kubuta ba su jin turanci sai kuma yanzu ga shi kuma akasarinsu na zangon karshe na kammala karatunsu a jami'a.

Palmatah ce kadai cikin su goma da ta samu damar samun gurbin karatu a wannan shahararriyar kwalejin bayan lauyan nan mai kare hakkin bil adama wato Emmanuel Ogebe ya dauki nauyin daliban zuwa kasar waje.

AFP

Asalin hoton, AFP

A watan Janairun 2016 ne, Palmatah tare da wasu da harin Boko Haram ya taba rutsawa da su wadanda ba 'yan matan Chibok bane suka fara karatunsu a wannan kwalejin.

Daya daga cikinsu tun a shekarar bara ta kammala digirin na ta a bangaren kimiyya inda ita ma Palmatah abin da ta samu kenan.

Abubuwan da suka faru

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Mayakan Boko Haram sun yi wa sakandaren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno tsinke a ranar 14 ga Afrilun 2014, suka kwashe dalibai 276.

Lokaci ne da ya shiga babin munanan abubuwan tarihi da jefa duniya cikin firgici da kaduwa.

Mako biyu bayan sace su ne, wasu mata suka fara gangami ta hanyar zanga-zanga, abin da ya zama mafari ga fafutukar neman a ceto 'yan matan Chibok mai taken #BringBackOurGirls.

A ranar 5 ga watan Mayu kuma, Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani faifan bidiyo ya fito ya amsa cewa su ne suka sace 'yan matan Chibok.

Kwamitin gano gaskiya da Burgediya Janar Ibrahim Sabo ya jagoranta ya ba da rahoto ranar 21 ga watan Yunin 2014, inda ya ce babu dalibar da aka ceto bayan 57 da suka kubuta tun farko.

Satar 'yan matan Chibok ta yi matukar jan hankalin al'ummar duniya, inda a ranar 14 ga watan Yuli fitacciyar matashiyar nan mai rajin bunkasa ilmin mata a duniya, Malala Yusoufzai ta ziyarci Najeriya.

Masharhanta da dama na ganin cewa al'amarin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan wanda aka kayar a zaben 2015.

Jim kadan da rantsar da shi kan mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin karya kashin bayan Boko Haram tare da alkawalin ceto 'yan matan Chibok.

Sai dai kimanin wata shida bayan wannan alkawari a ranar 14 ga watan Janairun 2016, Daruruwan iyayen 'yan matan Chibok suka yi wani maci a Abuja domin nuna juyayi bayan cika kwana 600 da sace 'yan matan Chibok.

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 19 ga watan Mayun 2016, rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa game da Amina Ali 'yar sakandaren Chibok ta farko da aka gano a yankin Damboa. An gan ta ne dauke da jariri.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuma a ranar 22 ga Satumba, ya gayyaci Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani don tattaunawa da Boko Haram ta yadda za a yi musayar 'yan matan Chibok.

Ba da dadewa ba kuma sai wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya shaida wa BBC ranar 13 ga watan Oktoba cewa an saki 'yan matan Chibok 21.

Bayan wata bakwai, a ranar 7 ga watan Mayun 2017 fadar shugaban Najeriya ta ce 'yan matan Chibok 82 da Boko Haram ta sako a ranar Asabar biyu ga wata, sun isa Abuja.

A ranar 14 ga Janairun bara, Dan jaridar nan mai ba da rahotanni kan kungiyar Boko Haram a Najeriya Ahmed Salkida, ya ce 'yan matan Chibok 15 kawai suka rage a raye cikin 112 da har yanzu ke hannun kungiyar.

Gwamnatin kasar dai ta yi watsi da wannan labari, inda ta ce har zuwa lokacin suna ci gaba da tattaunawa don ganin an saki ragowar 'yan matan.

Kwanaki bayan nan Boko Haram ta fitar da wani bidiyo dauke da wasu daga cikin ragowar 'yan matan Chibok. Bidiyon ya nuna daya daga cikin matan sanye da shudin hijabi da farin nikabi tare da wasu mata kimanin goma.

Kamar ba a dauki darasi kan sace 'yan matan Chibok ba, a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, Boko Haram ta kuma sace 'yan matan sakandare 110 a makarantarsu da ke Dapchi a jihar Yobe. Al'amarin ya sake jefa Nijeriya cikin rudani da tunanin 'yan matan Chibok.

Baya ga rukunin 'yan matan Chibok da aka kubutar, an kuma gano daidaikunsu a lokuta daban-daban. Salomi Pagu ita ce ta baya-bayan nan da aka gano ranar 5 ga watan Janairun 2018.