Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyar 'yan tawayen Yemen ta fara shirin janye dakarunta
'Yan tawayen Houthi na shirye-shiryen janyewa daga tashar jirgin ruwa ta Hudaydah da wasu kananan tashoshi a yankin a matsayin mataki na farko tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Disamba.
Duka bangarorin biyu wato na gwamnati da kuma na Houthi sun cimma yarjejeniyar barin tashar jirgin ruwan domin bayar da dama don shigo da kayayyakin tallafi.
Alamun janyewar sun fara bayyana ne a ranar Asabar inda aka ga 'yan tawayen Houthi na janye dakarunsu.
Ana sa ran janyewar dakarun daga tashar za ta dauki kwanaki hudu.
A kalla fararen hula 6,800 aka kashe a yakin basasar Yemen wanda aka shafe shekaru hudu ana gwabzawa.
Hakazalika yakin ya yi sanadiyar raunata mutum 10,700 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, har ila yau dubban mutane sun mutu sakamakon rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki da kuma cututtuka da rashin lafiya iri-iri.
Jakadan majalisar dinkin duniya na musaman a kasar Yemen Martin Griffiths ya shaida wa BBC cewa janye dakarun shi ne mataki na farko.
Ya kuma ce ''muna da aiki ja a gabanmu wajen tabbatar da cewa gwamnatin Yemen ta gamsu da wannan yunkuri.''
Me ya sa tashar jirgi ta Hudaydah ke da amfani?
Tashar jirgin ruwa ta Hudaydah ita ce kashin bayan kashi biyu cikin uku na 'yan kasar Yemen.
Rufe tashar a kwanakin baya ya jefa akasarin 'yan kasar cikin bala'i inda a yanzu haka da dama ke fama da karancin abinci da yunwa.
A karkashin yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta kulla tsakanin bangarorin biyu, duka bangarorin sun yarda sun su janye dakarunsu daga garin Hudaydah da kuma tashoshin na Hudaydah da suka hada da Salif da kuma Ras Issa.
Matakin da 'yan tawayen na Houthi suka dauka a halin yanzu na janye dakarunsu alama ce da ke nuna cewa yarjejeniyar ta fara aiki.
Tun a baya dai, Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta rarrashin bangarorin biyu da su bayar da dama domin a shiga wani makeken dakin ajiya da ke cike da hatsin da zai iya ciyar da mutane miliyan 3.7 a wata daya.
Ma'aikatan bayar da tallafi sun shafe kusan watanni biyar suna kokarin samun shiga dakin ajiyar amma abin ya ci tura.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadi da cewa hatsin zai iya lalacewa.