Kirkirar sabbin masarautu ba zai karya lagon masarutar Kano ba - Isa Sunusi

Ana cigaba da samu sabbin bayanai kan kirkirar masarautu a Kano

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana cigaba da samu sabbin bayanai kan kirkirar masarautu a Kano

Tsohon sakataren sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu wato Isa Sanusi ya ce rarraba masarautu da aka yi ba zai taba karya lagon masarautar Kano ba.

Malam Sunusi ya bayyana haka ne bayan gurfana da ya yi a ofishin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano don amsa wasu tambayoyi kan zargin facaka da kudaden masarautar.

Hukumar ta gayyaci shi ne tare da dan Buran din Kano Munir Sunusi, wanda shi ne shugaban ma'aikatan fadar sarkin, da akantan masarautar da kuma Falakin Kano Mujitaba Falaki.

An dai gayyaci wadannan mutane ne domin su yi bayanin kan zargin kashe kudaden masarautar ba bisa ka'ida ba.

A baya dai hukumar ta dakatar da wannan bincike, sai dai an sake waiwayensa a wannan karon.

Bincike na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Kano ta fara wani yunkuri na kirkiro karin masarautu, abin da wasu ke ganin hakan yunkuri ne na rage wa Sarki Sanusi karfin iko.

Bayan fitowarsa daga wajen binciken tsohon sakataren Isa Sanusi, wanda aka sauke saboda zargin zagon kasa, ya shaida wa BBC cewa yana goyon bayan binciken da ake yi.

Ya ce tambaya ce aka yi musu suka ba da amsa, sai kuma wasu bayanai da aka ba su su je su yi nazari a kai.

Malam Isa ya kuma nuna cewa duk da cewa su 'yan gida ne ba za su ki bincike ba domin abu ne mai kyau saboda za a fitar da gaskiya a kuma tantace.

Ya kuma ce rarraba masarautun da aka yi ba zai taba karya masarautarsu ba ''komai ka gani haka Allah ya kaddaro, Allah shi ne zamani kuma idan zamani ya zo da haka sai a karba a ci gaba da hakuri.''

Haka zalika ya musanta zarge-zarge da ake cewa yana hada kai wajen ingiza gwamnatin Kano.