Ramadan 2019: Musulmi sun fara azumi

Lokacin karatu: Minti 1

A Najeriya, mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III, wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ya bayyana ganin watan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Lahadi.

Wannan na zuwa ne bayan ganin jinjirin watan da aka yi a wurare daban-daban a fadin duniya.

Kwamitin ganin wata na Najeriya ya wallafa jawabin sarkin a shafin Twitter inda sarkin ya umarci jama'a da su tashi da azumi ranar Litinin.

Akasarin Musulmai a fadin duniya za su tashi da Azumin watan Ramadan ranar shida ga watan Mayun 2019 wanda hakan ya zo dai-dai da daya ga watan Ramadan 1440.

Sarkin ya yi kira da a yawaita ibada a cikin watan na Ramadan kuma a ci gaba da addu'a ga shugabanni.

Baya ga Najeriya Musulmai a wasu kasashen duniya irin su Saudiyya za su fara azumin na watan Ramadana a ranar Litinin.

Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi inda ake matsa kaimi kan ibada da addu'o'i.