Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa mata ke kunyar cin abinci idan ba sa azumi?
Mata musulmi a kafofin sada zumunta sun tattauna a kan kalubalen da suke fuskanta wajen cin abinci a lokacin azumi idan suna al'ada.
Wasu sun ce su kan buya daga idon 'yan uwansu maza domin ka da a gansu ko kuma su yi karya saboda suna jinin al'ada.
Sophia Jamil ta shaida wa BBC cewa: "Akwai wasu da ba sa son su bayyana wannan matsala saboda suna ganin a musulunce ba su kyauta ba, sai dai akwai matsala".
A lokacin watan Ramadan, musulmi ba sa cin abinci tun daga bullowar alfijir zuwa rana. Ko da yake mace mai al'ada ba ta azumi.
Sai dai duk da haka akwai wasu matan da suke jin kunyar bayyana cewa suna jinin al'ada har mutane su gane.
"Mahaifiyata kan fada min cewa, idan kin fara jini haila, ka da ki gayawa wani namji, mata ne kawai za su sani," in ji matashiyar mai shekara 21.
"Akan haka duk lokacin da na ke shan ruwa kuma na hango mahaifina na zuwa, zan ajiye kofin na bar wurin. Mahaifiyata na ajiye min abinci a cikin dakina kuma sai ta ce ka da na bari a san ina cin abinci."
Sophia wadda ke zaune a New York kuma yar asalin kasar Pakistan ce, ta ce: "A lokacin da dan uwana ya kama ni ina cin abinci sai ya zura man ido yana ta kallona. 'Yan uwana maza sun rika kokarin ganin cewa sun kama ni ina cin abinci domin na ji kunya.
"Na so a ce ina da kwarin gwiwar fada musu cewa wannan abu ba laifi ba ne, kuma addini ne ya bukaci na ajiye azumi saboda ba ni da tsarki."
Sophia ta ce ba kasafai ake magana a kan jinin al'ada ba saboda "kunya" kuma mahaifiyarta ba ta fada mata cewa za ta yi jinin haila ba idan ta balaga."
"A gani na ya kamata a kawar da al'adun da suke kawo tarnaki ga mata masu jinin haila da ke sa su suna jin kunyar magana idan suna yi.
"Ya kamata mu rika magana a kansa, kuma ina ganin mu ne za mu kawo sauyi," a cewarta.
Ka'idojin azumi
A lokacin azumi Musulmi ba sa cin abinci ko shan ruwa da kuma jima'i daga asuba zuwa faduwar rana.
Ana bukatar yin niyyah kafin daukar azumi. Ana yin niyyah ne ko a cikin dare kafin a yi barci ko kuma lokacin sahur.
An saukaka wa mata masu juna da biyu da masu tabin hankali ko rashin lafiya da kuma gajiyayu ko matafiya ko wadanda rayuwarsu ke cikin hadari idan ba su ci abinci ba daga yin azumi.
Sabreen Imtair, ta shaida wa BBC cewa ta so ta taimakawa mutane su rika magana a kan dabi'un al'umma kan jinin al'ada, kuma ta wallafa sako a shafin Twitter domin ta karfafa gwiwa mata wajan yin mahawara akai.
Ta ce: "iyalina ba su da matsala da abubuwa irin wadannan, sai dai wasu mata ba sa iya cin abinci a gaban 'yan uwansu maza a lokacin azumi da kazantar da suke ji da kuma kunya a lokacin jinin al'ada."
"Akwai tsangwama sosai," in ji matashiyar. "Jin kunya da kuma boye al'ada tamkar nuna wariya ce. Ya sauya salon tunanin da ake da shi akai."
Sai dai Sabreen ba ta fuskanci kalubale kamar sauran mata a lokacin azumi ba. Ta rika cin abinci da shan ruwa a lokacin azumi a gaban 'yan uwanta maza.
"Na je na sayi lemon kwalba. Dan uwana na azumi kuma ya tambayeni me yasa na yi haka? D ana fada masa cewa ina al'ada sai ya ce to ba komai."
Ko da yake, Sabreen na ganin akwai bukatar ganin cewa mata sun saki jiki wajen magana a kan jinin haila.
"Mahaifiyata ta nuna min yadda zan yi amfani da audugar al'ada sai dai ba ta nuna min yadda zan fadawa mutane cewa ina al'ada ba," in ji ta.
"A baya-baya nan ne na fara magana akai. Abu ne da ba a son ana magana akansa idan muna al'ada, ba laifi ba ne idan mu ka sauya haka."