An aurar da zawarawa 3000 a Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje lokacin da yake jawabi ya yin daurin auren
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje lokacin da yake jawabi ya yin daurin auren

A ranar Asabar 5 ga watan Mayun 2019 ne gwamnatin Kano ta aurar da zawarawa 3000 a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta biya kusan miliyan 30 a matsayin sadakin ma'auratan.

An gudanar da daurin auren ne a duka kananan hukumomin Kano 44.

Gwamna Abdullahi Ganduje shine waliyan angwayen shi kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu shine waliyyan amaren da aka daurawa aure wanda adadin su ya kai 3000- maza 1500 mata 1500 kenan.

Mai martaba sarkin Kano ya yin jawabi a lokacin daurin auren zawarawa 3000 da aka gudanar a fadin jihar Kano a Babban masallacin Juma'a dake Kano
Bayanan hoto, Mai martaba sarkin Kano ya yin jawabi a lokacin daurin auren zawarawa 3000 da aka gudanar a fadin jihar Kano a babban masallacin Juma'a da ke jihar.

Wasu daga cikin hotunan zawarawan da aka aurar da kayayyakinsu

Jerin kujeru da zawarawan za su amfana da su
Bayanan hoto, Jerin kujeru da zawarawan za su amfana da su
Katifu da gadaje na zawarawan da aka aurar
Bayanan hoto, Katifu da gadaje na zawarawan da aka aurar
BBC
Wasu daga cikin Angwaye bayan daurin auren
Bayanan hoto, Wasu daga cikin angwayen bayan daurin auren
Wasu daga cikin Amare bayan daurin auren
Bayanan hoto, Wasu daga cikin amaren bayan daurin auren