An saki Zainab Aliyu a Saudiyya

Bayanan bidiyo, Yadda muka ji da sakin 'yar uwata - Hajara Aliyu
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomin Saudiyya sun saki Zainab Aliyu a birnin Jeddah ranar Talata.

Babban sakatare a ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya Mustapha Suleiman ya tabbatar wa BBC wannan labarin.

Ya ce "an rubuta wa jami'an gwamnatin Saudiyya takardu kamar yadda aka tsara a harkokin diflomasiyya, ana ta bayanai."

"Kuma an nuna masu gaskiyar wadannan mutane da kuma irin kokarin da gwamnati ta yi daga nan gida wajen kama wadanda ake zargi cewa su ne suka sanya masu kwayoyi a jakunkuna," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "saboda haka wannan al'amari da Allah Ya warware ta hannun wadanda jami'ai da hukumomi kasashen biyu.

Zainab tare Jami'an Ofishin jakadancin Najeriya a birnin Jidda

Asalin hoton, Nigeria Ministry of Foreign Affairs

Bayanan hoto, Zainab tare da Jami'an ofishin jakadancin Najeriya a birnin Jeddah

Daga nan ya yi godiya ga hukumomin Saudiyya dangane da hadin kan da suka ba su a kan "wannan al'amari mai wuyar warwarewa."

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafafan sada zumunta Bashir Ahmed ya bayyanaa hakan a shafinsa na Twitter.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A safiyar Talata wasu dalibai suka fara gudanar da zanga-zanga don neman a sake ta.

Daliban, wadanda akasari abokan karatunta ne a jami'ar Yusuf Maitama Sule, sun nemi a sake ta ba tare da wani ba ta lokaci ba.

An fara zanga-zangar ne daga Jami'ar tuna wa da Yusuf Maitama Sule a Kofar Nasarawa.

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari'a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu.

Jami'an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma 'yar uwarta Hajara.

Me 'yan Najeriya ke cewa?

Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon zanga-zangar neman sakin Zainab a Kano

'Yan Najeriya da dama ne a 'yan kwanakin nan suka cika shafukan sada zumunta da kiraye-kiraye ga hukumomi da a yi wa Zainab adalci.

Sun yi amfani da maudu'ai kamar #FreeZainab #JusticeForZainab a shafin Twitter.

Hukumar kare hakki ta Amnesty International ma ta yi irin wannan kira.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wasu dalibai da suka yi ikirarin abokan karatunta ne a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano sun ce za su gudanar da zanga-zangar lumana ta nemar wa Zainab adalci.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4