Zainab Aliyu: Najeriya ta dauki lauyoyi don kare ta

Kano
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Najeriya ta dauki lauyoyin da za su yi aikin wanke Zainab Aliyu daga zargin safarar kwayoyi da Saudiyya take yi mata.

Bashir Ahmad mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan kafafen sada zumunta ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

A yanzu haka Zainab na tsare a kasar Saudiyya bayan da jami'an tsaro suka kama ta jim kadan bayan isa kasar don yin aikin Umara.

Bashir ya ce: "Yayin da Shugaba Buhari ya umarci Abubakar Malami ya shiga lamarin Zainab, hukumar aikin hajji ta kasa ta bayar da sanarwar daukar lauyoyi don kubutar da Zainab daga zargi a kasar Saudiyya".

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A safiyar Talata wasu dalibai suka fara gudanar da zanga-zanga don neman a sake ta.

Daliban, wadanda akasari abokan karatunta ne a jami'ar Yusuf Maitama Sule, sun nemi sake ta ba tare da wani ba ta lokaci ba.

An fara zanga-zangar ne daga Jami'ar tuna wa da Yusuf Maitama Sule a Kofar Nasarawa.

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari'a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu.

Jami'an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma 'yar uwarta Hajara.

Kano

Sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Amma tuni hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa wasu ma'aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) suka saka mata kwayar a jakarta.

Kano

Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.

Presentational grey line
Presentational grey line

Uku daga cikinsu ma'aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma'aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jmai'an tsaro ne a filin jirgin saman.

Hukumomin Saudiyya dai suna zartarwa wadanda suka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar hukuncin kisa ne.

Mataimakiya ta musamman ga Shugaba Buhari kan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce shugaban ya umarci Abubakar Malami da ya shiga maganar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

"Buhari ya umarci ministan shari'a da ya yi dukkanin mai yiwuwa don ganin an yi wa Zainab adalci. Mahaifinta ne ya sanar da mu kuma muna samun ci gaba game da ita da sauran mutum biyun," kamar yadda Abike Dabiri ta bayyana.

Wannan ya biyo bayan maganar da Sanata Shehu Sani ya yi ne, inda yake shawartar iyayen Zainab da su kawo kokensu gaban majalisar dokokin kasar domin ta shiga lamarin.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Dabiri ta kuma shaida wa jaridar Premium Times cewa Buhari ya shiga lamarin a lokacin da ya samu labari mako biyu da suka gabata.

Me 'yan Najeriya ke cewa?

'Yan Najeriya da dama ne a 'yan kwanakin nan suka cika shafukan sada zumunta da kiraye-kiraye ga hukumomi da a yi wa Zainab adalci.

Sun yi amfani da maudu'ai kamar #FreeZainab #JusticeForZainab a shafin Twitter.

Hukumar kare hakki ta Amnesty International ma ta yi irin wannan kira.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Wasu dalibai da suka yi ikirarin abokan karatunta ne a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano sun ce za su gudanar da zanga-zangar lumana ta nemar wa Zainab adalci.

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6