Amnesty: 'Ana lalata da mata da kananan yara a gidan yarin Maiduguri'

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaro da lalata da fursunoni musamman mata da kananan yara a birnin Maidugurin jihar Borno.

Kungiyar ta ce wani tsohon fursuna ya shaida mata cewa sojoji na yawan lalata da mata da kananan yara, wadanda ake tsare da su bisa zargin alaka da Boko Haram.

Yara 68 ne ake tsare da su a gidan yarin Maiduguri mai tsananin tsaro da Giwa Barracks, ciki har da wasu guda uku da ke jiran hukuncin kisa, in ji Amnesty.

Wasu tsofaffin fursunoni mata guda 15 sun shaida wa kungiyar cewa sojoji sun rika yi masu fyade tare da alkawarin nema masu 'yanci.

BBC ta tuntubi mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, inda ya ce za a yi bincike.

Ya bayyana cewa akwai kwamiti na musamman da aka kafa kan zarge-zargen, kuma zai bayyana sakamkon bincikensa ba tare da bata lokaci ba.

Karanta wasu karin labarai: