'Kishi da kwadayi ne babbar matsalar mata'

Wata malamar jami'a a arewacin Najeriya ta gabatar da wata lacca a shafin Facebook kan batun auren mace fiye da daya a wani bangare na bukin ranar mata ta duniya da za a yi ranar Juma'a.

Batun karin aure dai batu ne mai jawo kace-nace tsakanin mata da kuma ma'aurata a yankin.

BBC ta tambayi Malama Nafisa Abubakar Zaki ko mene ne wannan lakcar ta mayar da hankali a kai?