Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amnesty na son ruguza Najeriya ne - Sojojin Najeriya
Kungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da ruruta wutar rikicin manoma da makiyaya saboda gazawar da ta yi wajen bincike da hukunta wadanda ke aikata laifuka.
Rahoton da Amnesty ta fitar ya bayyana yanayin kashe-kashen da ya auku a tsakanin manoma da makiyaya a jihohin Adamawa da Binuwai da Taraba da Kaduna da kuma Filato.
Rahoton ya kuma zargi hukumomin da laifin kin hukunta masu laifi, lamarin da ya janyo mutuwar mutum kimanin 3,641 daga watan Janairun 2016 zuwa na Oktobar 2018.
Kungiyar ta kuma ce tana da hujjoji da ke nuna cewa sojojin kasar sun ki daukar matakin da ya dace duk da yake a yawancin lokuta suna kusa da inda rikicin ke aukuwa.
Rahoton ya janyo martani mai zafi daga rundunar sojojin Najeriya wadda ta ce kungiyar na kokarin yi wa kasar zagon kasa ne.
A wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya sanyawa hannu, rundunar sojojin Najeriya ta kuma nemi da a kori kungiyar daga Najeriya idan ta ci gaba da abin da ta kira rashin hankalin da ta ke nunawa.