Bala Mohammed: EFCC ta gurfanar da zababben gwamnan jihar Bauchi

Asalin hoton, Facebook
Hukumar EFCC da ke yaki da rashawa a Najeriya ta gurfanar da zababben gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed a gaban wata babbar kotu da ke Abuja ranar Litinin.
Sai dai zaman kotu bai yiwu ba saboda Alkalin kotun Yusuf Halilu bai samu halarta ba don aikace-aikacen da yake a kotun sauraren kararrakin zabe ta garin Abeokuta a jihar Oyo, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
EFCC ta gurfanar da tsohon ministan Abujan ne bisa zarginsa da karbar toshiyar-baki na wani gida a Abuja da aka kiyasta cewa kudinsa ya kai naira miliyon 500 lokacin da yake rike da mukamin ministan Abuja.
Sai dai Bala Mohammed ya musanta zargin.
Amma daga bisani, an ga zababben gwamnan zauren taron bitar da aka shirya wa a Abuja ranar Litinin.
A watan Maris ne hukumar zabe INEC ta bayyana Sanata Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi, bayan doke Gwamna Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC.
A shekarar 2017 ma wata babbar kotun Abuja, ta tura Bala Mohammed zaman gidan wakafi a gidan yarin Kuje saboda zargin cin hanci da rashawa.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya a kan zarge-zarge shida da suka shafi cin hanci a lokacin da yake kan mulki.
Ana zarginsa da karbar cin hancin N550 million, zargin da ya musanta.
Sai dai daga baya an ba da belinsa.











